in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan kabilar Dolan sun nuna kauna sosai ga kide-kiden Muqam
2010-12-28 10:08:10 cri

Wakar da kuke saurara yanzu wani babi ne mai taken "Bash Bayawan" da ke cikin kide-kiden gargajiya na Muqam na kabilar Uygur ta jihar Xinjiang da ke arewa maso yammacin kasar Sin, inda aka rera wakar kamar haka:"Ku je ku gai da masoyiyata, ku gaya mata halin da nake ciki. Idan tana so ta fahimci yadda nake ji a rai, to ku gaya mata cewa, ina cikin koshin lafiya kuma na ji dadin zama rayuwata."

Kide-kiden Muqam na kabilar Uygur ta jihar Xinjiang wata irin dukiya ce ta fasaha da ta hada kide-kide da raye-raye da wake-wake waje guda, don haka a kan kira shi "tushen kide-kiden kabilar Uygur" da kuma "uwar kide-kiden kabilar Uygur". A cikin shekaru fiye da 600 da suka gabata, 'yan kabilar Uygur sun gaje shi daga zuriya zuwa zuriya, wanda aka mai da shi kamar wani littafin addini na kide-kide. A matsayinta ta wani muhimmin reshe na kabilar Uygur, 'yan kabilar Dolan suna zaune ne a gundumar Awat da kuma wuraren da ke arewa maso yammacin kwarin Tarim, kide-kiden Muqam kuwa wani muhimmin sashe ne na zaman rayuwarsu wanda ba a iya rabawa, don haka kide-kiden Muqam na kabilar Dolan ya kasance daya daga cikin muhimman rukunoni na kide-kiden Muqam na kabilar Uygur.

Waka mai taken "Bash Bayawan" da kuka saurara dazu wata karamar kungiyar kide-kiden Muqam ce ta gabatar muku, wadda ta kunshi tsoffin masu fasaha fiye da 10 daga gundumar Awat. A cikinsu kuwa, masu karantan shekaru sune wadanda suka zarce shekaru 40 da haihuwa, sannan wanda ya fi tsoho kuma shekarunsa sun zarce 80 a duniya. Mr. Abdulkadir dan kabilar Uygur mai shekaru 66 da haihuwa shi ne shugaban kungiyar nuna kide-kiden Muqam. Kamar yadda masu buga fiyano da ke cikin kungiyar wake-wake masu farin jini ke yi, wannan tsoho mai kwarjini sosai da ya buga kayan kida mai suna Qalun shi ya jagoranci tsarin kidan baki daya.

An haifi Abdulkadir ne a cikin wani gidan zuriyoyin makadan Muqam na kabilar Dolan da ke gundumar Awat. Iyayensa sun san juna da kuna nuna wa juna soyayya ta hanyar kide-kiden Muqam. Yanzu Mr. Abdulkadir ya ci gaba da bin taken iyayensa da kuma zama wani makadin Muqam. Yayin da yake bayani game da asalin gidansu, Mr. Abdulkadir ya yi alfahari sosai. Kamar yadda yake cewa, "mahaifina wani kwararre ne a fannin kide-kiden Muqam, mahaifiyata da kuma kawuna su ma sun shahara a kide-kiden Muqam. Dukkan iyalinmu sun iya kide-kiden Muqam, kuma sun koya mini fasahar kide-kiden. Yanzu dai, ina da 'ya'ya maza hudu, uku daga cikinsu sun iya buga kayan kidan Qalun. Dukkan iyalina suna iya wasannin fasaha, kowa na da fanni na musamman da ya kware a kai. Ana iya samun kayayyakin kida iri daban daban a gidanmu. Dukkan iyalinmu muna iya wake-wake da raye-raye a lokacin da aka yi baki domin nuna musu maraba."

Mr. Abdulkadir ya gudanar da ayyukan da suka shafi kide-kide har na tsawon kusan shekaru 55 bayan da ya fara koyon kidan Qalun yayin da shekarunsa suka kai 12 da haihuwa. Yanzu ba ma kawai Mr. Abdulkadir ya kware sosai a fannin buga kayan kidan Qalun ba, hatta ma yana da kwarewa a fannonin buga kayan kidan Rawap da na Gajak da na mindiri, kana ya iya raye-raye sosai. Amma abin da ya shige zukatan mutane shi ne a hakika dai, wannan kwararre ba shi da ilmin kide-kide ko kadan. Kamar yadda ya iya karanta Alkur'ani yadda ya kamata ko da bai fahimci harshen Larabci ba, Mr. Abdulkadir da ba shi da ilmin kide-kide ya iya kide-kiden Muqam tamkar kabari. Dalilin da ya sa haka shi ne sabo da namijin kokarin da ya yi wajen koyon kide-kiden Muqam a cikin shekaru fiye da 50 da suka gabata, kana da fahimtar da yake da ita kan kide-kiden Muqam. Kamar yadda ya fada, "A lokacin da nake karami, na fara koyon yadda ake sarrafa wadannan kayayyakin kide-kide, kuma na yi ta yi har zuwa yanzu. Dalilin da ya sa haka shi ne sabo da kide-kiden Muqam na kabilar Dolan sun sha bamban sosai da na sauran kasashe, ba za a iya nuna su yadda ya kamata ba sai dai amfani da kayayyakin kida na kabilarmu."

Tun daga karni na 16 lokacin da Amannisahan, matar yarimar daular Yarkand ta fara tattara kide-kiden Muqam a karon farko, har zuwa yanzu ko da yaushe a kan gaji kide-kiden Muqam ta baki daga malamai zuwa dalibai. A halin yanzu dai, Mr. Abdulkadir yana bin wannan al'adar gargajiya yana koyar da wannan fasaha ga zuriyarsa. Sakamakon ci gaban tattalin arzikin jihar Xinjiang da kuma tsarin bude kofarta, matasa 'yan kabilar Dolan sun fara amfani da wasu kayayyakin kida na kasashen waje yayin da suke kokarin rike gadon wannan dukiyar fasaha, Emetcan, babban dan Mr. Abdulkadir ya yi haka. Yayin da yake bayani kan abubuwan da ya koya, ya gaya wa wakiliyarmu cewa, "Na iya amfani da kayan kida na Qalun da na Rawap na kabilar Dolan da na Rawap na yankin Kashgar da na Tanbur da na Duttar. Ban da wannan kuma na iya kada guitar da accordion, wadanda har ma mahaifina bai iya ba."

Ko da yake Emetcan ya iya sarrafa kayayyakin kida da dama, amma ya ce ba shi da kwararewa a fannin kide-kiden Muqam, ba kamar mahaifinsa ba Emetcan ya kara da cewa, "Mahaifina ya fi kwarewa a fannin nuna kide-kiden Muqam."

Ban da wannan kuma Emetcan ya furta cewa, yanzu 'ya'yansa maza biyu sun fara koyon kide-kiden Muqam sakamakon tasirin da iyalinsu ke bayarwa a wannan fanni, kakansu wato Mr. Abdulkadir shi ma ya kan koya musu fasahar buga kayayyakin kida iri daban daban.

A kokarin da ake kara kiyaye kide-kiden Muqam, an kafa cibiyar gadon al'adun kabilar Dolan a shekara ta 2006 a gundumar Awat. A matsayinsa na wanda ke rike gadon kide-kiden Muqam na kabilar Dolan, Mr. Abudlkadir ya dauki nauyin horar da dalibai biyu a ko wace shekara, sakamakon haka kuma yana samun kudin alawus Yuan 3600 a ko wace shekara.

Bayan da aka shigar da kide-kiden Muqam na kabilar Uygur na jihar Xinjiang ta kasar Sin cikin jerin sunayen kayayyakin tarihi na al'adu na kungiyar ilmi da kimiyya da al'adu ta MDD wato UNESCO da kuma na matakin kasar Sin, a halin yanzu dai, yawan iyalan makadan Muqam na gundumar Awat kamar Mr. Abdulkadir ya zarce 400. Bugu da kari kuma matasa 'yan kabilar Dolan masu dimbin yawa sun fara nuna himma da kwazo a sha'anin kiyaye da gadar kide-kiden Muqam, a kokarin yada wannan fasaha ta kabilar Uygur ta jihar Xinjiang daga zuriya zuwa zuriya bisa namijin kokarin da suke yi

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China