Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
 
• Ziyarar da firayin ministan kasar Sin Wen Jiabao ya yi a kasashen Afirka ta sami sakamako da yawa 2006-06-26
A ran 25 ga wata, Mr. Wen Jiabao firayin ministan kasar Sin ya dawo gida bayan ya yi ziyara a kasashe 7 na Afirka. A cikin kwanaki 8 da suka wuce, firaminista Wen Jiabao ya yi ziyarar a kasashen Masar, Ghana, Kongo Brazzaville, Angola, Afirka ta kudu, Tanzania da Uganda bi da bi, ya aika da abokantaka ta jama'an kasar Sin ga...
• Zantutukan da Mr Li Zhaoxing ya yi a kan ziyarar da Mr Wen Jiabao ya yi a kasashe 7 na Afrika 2006-06-25
Daga ran 17 zuwa ran 24 ga wannan wata, firayim ministan kasar Sin Wen Jiabao ya yi ziyarar aiki a kasashe 7 na Afrika, wato kasar Masar da Ghana da Kongo Kinshasha da Angola da Afrika ta kudu da Tanzaniya da Uganda. Bayan ziyarar, ministan harkokin waje na kasar Sin...
• Firayin ministan kasar Sin ya nuna ta'aziyya ga masanan kasar Sin wadanda suka mutu a kasar Tanzania 2006-06-24
A ran 23 ga wata da safe, agogon kasar Tanzania, a karkashin rakiyar takwaransa na kasar Tanzania Edward Lowassa, firayin minista Wen Jiabao na kasar Sin wanda ke yin ziyara a kasar Tanzania ya je wurin kaburburan da ke karkarar birnin Dares Salam na kasar Tanzania, inda ake binne masanan kasar Sin wadanda suka mutu lokacin da suke aiki a kasar Tanzania.
• Ya kamata a kara raya sabuwar dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakanin Sin da kasashen Afirka 2006-06-22
A ran 22 ga wata, firayin minista Wen Jiabao na kasar Sin wanda ke yin ziyara a kasashen Afirka ya halarci kuma ya bayar da wani jawabi a gun taron dandalin fadin albarkacin bakinka kan cinikayyar da ake yi a tsakanin Sin da kasar Afirka ta kudu da aka shirya a wannan rana a birnin Cape Town, babban birnin kafa dokoki na kasar Afirka ta Kudu
• Idan akwai aboki nagari, kome nisansa, tamkar a kusa yake 2006-06-21
A ran 20 ga wata da safe, agogon wurin, firaministan kasar Sin, Wen Jiabao ya kai ziyara a makarantar Brazza da ke birnin Brazzaville, babban birnin kasar Congo Brazzaville. Wannan babbar makaranta kuma ta shahara ne sabo da darrusan Sinanci da take koyarwa. A ran nan, makarantar cike take da doki sabo da ziyarar firaministan kasar Sin.
• Firaministan kasar Sin ya halarci bikin kammala aikin hanya a kasar Ghana
 2006-06-20
A ran 19 ga wata, tare da shugaba Kufuor na Ghana ne, firaministan kasar Sin, Wen Jiabao, wanda a lokacin ke yin ziyara a kasar Ghana, ya halarci bikin kammala aikin gyara da fadada wata hanyar mota ta Ghana da gwamnatin kasar Sin ta ba da taimako ga wannan aiki. Sabo da haka, yanzu sai ku saurari wani rahoton da wakilanmu suka aiko mana daga bikin.
• Bayanin Mr Wen Jiabao a kan dangantaka a tsakanin Sin da Afrika da kuma hadin guiwarsu 2006-06-19
A ran 18 ga wata, Mr Wen Jiabao, firayim ministan kasar Sin ya yi bayani a kan batutuwan da suka shafi dangantaka da ke tsakanin Sin da Afrika da kuma hadin guiwarsu daga duk fannoni, a gun taron manema labaru da aka shirya a birnin Alkahira a karshen ziyararsa a kasar Masar.
• Wakokin yaba zumunci a tsakanin Sin da Masar suna yaduwa a gaban Pyramid na kasar Masar 2006-06-18
A ran 17 ga wata da dare, a bakin kogin Nile, kuma a gaban Pyramid inda suke birnin Alkahira na kasar Masar, an shirya shagalin murnar cikon shekaru 50 da kafuwar dangantakar diplomasiyya a tsakanin Sin da Masar
• Sin da Afrika sun shiga sabon lokacin hadin kansu a duk fannoni, in ji kwararren kasar Sin 2006-06-17
Shekarar nan ita ce zagayowar shekaru 50 da aka fara kulla huldar diplomasiya a tsakanin Sin da kasashen Afrika. Malam Wang Hongyi, kwararren kasar Sin a fannin harkokin Afrika kuma mataimakin shugaban ofishin nazarin harkokin Afrika na cibiyar nazarin harkokin duniya ta kasar Sin ya bayyana a kan wannan cewa, a cikin shekarun nan 50 da suka wuce, kasar Sin da kasashen Afrika sun taba kai hadin guiwarsu a fannin siyasa da tattalin arziki zuwa wani sabon mataki har sau biyu