A ran 20 ga wata da safe, agogon wurin, firaministan kasar Sin, Wen Jiabao ya kai ziyara a makarantar Brazza da ke birnin Brazzaville, babban birnin kasar Congo Brazzaville. Wannan babbar makaranta kuma ta shahara ne sabo da darrusan Sinanci da take koyarwa. A ran nan, makarantar cike take da doki sabo da ziyarar firaministan kasar Sin.
Tun daga nesa ne wakilan kasar Sin suka ji kide-kide masu kayatarwa. Ashe, malamai da dalibai na makarantar Brazza ne suke wake-wake da raye-raye don yin maraba da firaministan kasar Sin da tawagar wakilan gwamnatin kasar Sin. Makarantar Brazza babbar makaranta ce da ta fi girma a kasar Congo Brazzaville, inda dalibai sama da dubu 4 ke dalibta. Tun daga shekara ta 1990, malamai biyu suka fara koyar da Sinanci a duk ajujuwa 3 na wannan babbar makarantar sakandare, a halin yanzu dai, gaba daya akwai dalibai 158 da suke karanta Sinanci a nan. Bisa rakiyar malaman wannan makaranta, Mr.Wen ya je aji na farko na mataki na uku na wannan makaranta, sai kawai ya ga da Sinanci ne aka rubuta 'mu gada ce ta kulla zumunta a tsakanin Congo da Sin' a kan allo. Da Sinanci ne daliban wannan aji suka yi marhabin da bakin nan da suka zo daga can nisa na kasar Sin.
'muna matukar doki sabo da zuwanka. Malamanmu sun koya mana cewa, kasar Sin kasa ce da ke da dogon tarihi da kuma al'adu masu albarka. Yau, ka zo wajenmu, ka kawo mana zumuncin jama'ar Sin ga jama'ar Congo Brazzaville.'
Ko da yake lafazin wadannan dalibai ba daidai yake sosai ba, amma fuskokinsu cike suke da sahihanci. wadannan dalibai da ke koyon Sinanci da malaman da ke koyar da Sinanci a nahiyar Afirka wadda ke da matukar nisa da kasar Sin, sun burge firaminista Wen, da sahihin zuci ne Mr.Wen shi ma ya ce wa dalibai, 'ina fatan za ku iya Sinanci kuma ku zo kasar Sin.'
Daga baya kuma, Mr.Wen ya dauki alli, ya je gaban allo, ya rubuta 'idan akwai aboki nagari, komin nisansa, tamkar a kusa yake'. Wannan fa shahararriyar jimla ce ta wani shahararren mawakin gargajiya mai suna Wang Bo na kasar Sin.'wannan waka ta bayyana cewa, ko da yake akwai nisa sosai a tsakanin Sin da Afirka, amma duk da haka, tamkar makwabta ne suke ga juna.'
Yayin da Mr.Wen ya fita daga aji, sai da Sinanci ne malamai da dalibai dubai na wannan makaranta suka ce, 'sannu! Sannu!'
ko da yake wannan ziyara gajeriya ce, amma ta bayyana zumuncin jama'ar Congo Brazzaville ga jama'ar kasar Sin. An kuma gane cewa, kome nisan da ke tsakanin kasashen biyu ba zai iya dakatar da zumuncin da ke tsakaninsu ba.(Lubabatu Lei)
|