A ran 18 ga wata, Mr Wen Jiabao, firayim ministan kasar Sin ya yi bayani a kan batutuwan da suka shafi dangantaka da ke tsakanin Sin da Afrika da kuma hadin guiwarsu daga duk fannoni, a gun taron manema labaru da aka shirya a birnin Alkahira a karshen ziyararsa a kasar Masar.
Mr Wen Jiabao ya kara da cewa, yau sama da shekaru 50 ke nan da kulla hadin guiwa a tsakanin Sin da Afrika. Ko a lokacin da kasar Sin ta kasance cikin mawuyacin hali sosai ma, ta yi duk abubuwa da take iya yi wajen nuna goyon baya da gudummowa ga jama'ar kasashen Afrika daban daban a cikin rabin karni da ya wuce. Yawan kudin gudummowa da kasar Sin ta bai wa kasashen Afrika a fannoni daban daban ya kai kudin Sin Yuan biliyan 44.4 a cikin shekarun nan 50 da suka wuce, kuma ta yi manyan ayyuka da ayyukan jin dadin jama'a da yawansu ya kai kimanin 900 a Afrika. Haka zalika kasar Sin ta aika da kungiyoyin likitocinta zuwa kasashen Afrika 43, 'yan kungiyoyin nan wadanda yawansu ya kai dubu 16, sun ba da magani ga wadanda suka ji raunuka da masu fama da cututtuka da yawansu ya kai miliyan 240.
Mr Wen Jiabao ya kara da cewa, "kasar Sin tana dora matukar muhimmanci ga bunkasa hulda da ke tsakaninta da kasaashen Afrika a fannin tattalin arziki da ciniki. Muna gudanar da manufofi uku game da bunkasa huldar nan. Na daya, kasar Sin za ta yi kokari sosai wajen shigo da hajjoji daga kasashen Afrika, kuma za ta dauki matakai wajen sa kaimi ga kasashen Afrika da su yi tallar hajjojinsu. Na biyu, kasar Sin za ta hada aikin ba da gudummowar tattalin arziki da ta fasaha a lokaci guda, musamman ta taimaki kasashen Afrika wajen samun kwararewa don raya su su da kansu. Na uku, za ta yi kokari sosai wajen horar da 'yan fasana da jami'an gudanarwa domin kasashen Afrika. "
Bayan haka Mr Web Jiabao ya ci gaba da cewa, a gun taro na karo na biyu na dandalin tattaunawa kan hadin guiwa tsakanin Sin da Afrika da aka kira a birnin Addis Ababa, hedkwatar kasar Habasha yau da shekaru uku da suka gabata, mun taba gabatar da cewa, kasar Sin za ta horar da 'yan fasaha irin daban daban da yawansu zai kai dubu 10 domin kasashen Afrika, to, za mu cim ma wannan manufar a shekarar nan.
Mr Wen Jiabao ya ce, za a sake shirya taron dandalin tattaunawa kan hadin guiwa tsakanin Sin da kasashen Afrika da taron koli na Sin da Afrika a watan Nuwamba mai zuwa, inda gwamnatin kasar Sin za ta mai da hankali sosai ga rage basussuka da take bin kasashen Afrika, da ba da gudummowar tattalin arziki, da horar da kwararru da zuba jari da masana'antun kasar Sin ke yi da dai sauransu.
Da ya tabo magana a kan matsayin kasar Sin kan dangantaka a tsakanin Sin da kasashen Afrika da hadin guiwarsu, sai Mr Wen Jiabao ya ce, "kullun gwamnatin kasar Sin tana gudanar da manufofin girmama juna da zaman daidaici don moriyar juna da rashin yin shisshigi cikin harkokin gida na sauran kasashe. Mun hakake, yankuna daban daban da jama'ar kasashe daban daban su iya daidaita batutuwansu su da kansu. Kasar Sin tana son ganin ci gaba da kasashen Afrika ke samu wajen bunkasa tattalin arzikinsu, da tabbatar da zaman karko da na jintuwa, da kyautata tsarin dimokuradiyya da na shari'a, da inganta jin dadin rayuwar jama'a."
Bayan haka Mr Wen Jiabao ya jaddada cewa, kasar Sin ba za ta manta da goyon baya mai daraja da jama'ar Afrika suka nuna wa kasar Sin a cikin wani tsowon lokaci da ya wuce ba. Ya ce, "bai kamata mu manta da abubuwa nagari da aka yi mana ba, sa'an nan kuma bai kamata mu manta da yin abubuwa nagari domin saura ba" (Halilu)
|