Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-24 18:02:11    
Firayin ministan kasar Sin ya nuna ta'aziyya ga masanan kasar Sin wadanda suka mutu a kasar Tanzania

cri

A ran 23 ga wata da safe, agogon kasar Tanzania, a karkashin rakiyar takwaransa na kasar Tanzania Edward Lowassa, firayin minista Wen Jiabao na kasar Sin wanda ke yin ziyara a kasar Tanzania ya je wurin kaburburan da ke karkarar birnin Dares Salam na kasar Tanzania, inda ake binne masanan kasar Sin wadanda suka mutu lokacin da suke aiki a kasar Tanzania. San nan kuma ya yi rangadin aiki a filin wasannin motsa jiki na kasar Tanzania domin gai da ma'aikatan kasar Sin da na kasar Tanzania wadanda suke gina wannan filin motsa jiki. Gwamnatin kasar Sin ce ta samar da taimakon kudi domin gina shi. Yanzu ga wani bayanin musamman da wakiliyarmu ta aiko mana daga Dares Salam.

Da farko dai, a karkashin rakiyar Edward Lowassa, firayin ministan kasar Tanzania, Mr. Wen Jiabao ya tafi muhimmin kabarin inda ake da kalmomi "Kabari ne Masanan kasar Sin", ya ajiye furannin jana'izza, kuma ya bayar da jawabi cewa, "Yau da shekaru fiye da talatin da suka wuce, wasu Sinawa nagarta sun sha tafiya sun isa nahiyar Afirka tare da nauyin da aka dora musu. Sun sha wahaloli iri iri sun hada da jama'ar kasar Tanzania masu yin aikin wurjanjan kuma masu jarumtaka sun shimfida wata hanyar dogo irin ta zamani a nahiyar Afirka. A sa'i daya kuma, wasu daga cikinsu sun riga mu gidan gaskiya a wurin da ke nisa da garinsu sosai. Yau, mun zo nan mun mika su furanni domin bayyana tunaninmu."

Wen Jaibao ya ce, ko da yake lokaci yana wucewa cikin sauri, amma, kasa mahaifarsu da jama'ar kasar Tanzania ba za su manta da mutane wadanda suka ba da gudummawa sosai wajen sada zumunta a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka kuma har abada.

Mr. Lowassa ma ya bayyana girmamawa ga mutanen kasar Sin wadanda suka mutu lokacin da suke shimfida hanhar dogo da ke hade da Tanzania da kasar Zambia. "Gudummawar da suka bayar ta ciyar da tattalin arziki da zaman al'umma na kasar Tanzania da kasar Zambia gaba. A sa'i daya kuma, ta ciyar da kasashen da ke tsakiyar Afirka da kasashen da ke kudancin Afirka gaba. Wannan hanyar dogo ta fi sauran hanyoyin dogo muhimmanci domin wannan hanyar dogo tamu ce. Ko da yake kasar Sin ce ta samar da taimako wajen shimfida wannan hanyar dogo, amma lokacin da mutanen kasar Sin suke shimfida wannan hanyar dogo, ba su yi tsammani cewa wannan hanyar dogo ce ta kasar Sin ba."

An binne masana da kwararru da kwadago 69 na kasar Sin wadanda suka mutu lokacin da suke aiki a kasar Tanzania a wurin kaburburan domin ba da gudummawa ga bunkasuwar kasar Tanzania. Mutane 47 daga cikinsu sun rasu ne lokacin da aka shimfida hanyar dogo da ke hade da Tanzania da Zambia da tsawonta ya kai fiye da kilomita 1860.

San nan kuma, Wen Jiabao ya yi rangadin aiki a filin wasannin motsa jiki na kasar Tanzania. Gwamnatin kasar Sin ce ta ba da taimako domin gina wannan filin wasannin motsa jiki inda ke da kujeru dubu 60. An fara gina shi a shekarar 2005. Bisa shirin da aka tsara, a watan Janairu na shekara ta 2007 ne za a gama aikin gina shi. Wen Jiabao ya gai da ma'aikatan kasar Sin da na kasar Tanzania wadanda suke aiki a wurin gina filin wasannin motsa jiki. Wen ya ce, "Filin wasannin motsa jiki na kasar Tanzania muhimmin ayyuka daban da kasashen Sin da Tanzania suke gina tare. Injiniyoyin kasar Sin da na kasar Tanzania kuna aiki tare kuna bayar da namijin kokarinku kan yadda za a kammala wannan ayyuka cikin lokaci tare da tabbatar da ingancin wannan ayyuka."

Injiniyoyi da ma'aikata kimanin daruruwa na kasar Sin da na kasar Tanzania wadanda suke wurin sun yi tafi sosai domin jawabin da Mr. Wen ya fadi. Injiniyoyin kasar Sin sun bayyana cewa, za su yi namijin kokarinsu domin kammala wannan ayyuka cikin lokaci tare da inganci, kuma za su ci gaba da bayar da gudummawarsu wajen sada zumunta a tsakanin kasar Sin da kasar Tanzania.   (Sanusi Chen)