Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-18 19:06:05    
Wakokin yaba zumunci a tsakanin Sin da Masar suna yaduwa a gaban Pyramid na kasar Masar

cri
A ran 17 ga wata da dare, a bakin kogin Nile, kuma a gaban Pyramid inda suke birnin Alkahira na kasar Masar, an shirya shagalin murnar cikon shekaru 50 da kafuwar dangantakar diplomasiyya a tsakanin Sin da Masar. Wen Jiabao, firayin ministan kasar Sin wanda ke yin ziyara a kasar Masar, da Ahmed Nazif, takwaransa na kasar Masar da sauran baki wadanda suke yunkurin sada zumunta a tsakanin Sin da kasar Masar sun halarci wannan shagali. Yanzu ga wani bayanin musamman da wakilanmu suka aiko mana daga birnin Alkahira.

Gidan rediyo mai hoto na tsakiya na kasar Sin da ofishin jakadancin kasar Sin da ke kasar Masar kuma da gidan rediyo mai hoto na farko na kasar Masar sun shirya wannan shagali tare. Yang Kaili, babban direktan wannan shagali wanda ya zo daga gidan rediyo mai hoto na tsakiya na kasar Sin ya gaya wa wakilanmu cewa, "Wannan ne karo na farko da aka shirya irin wannan shagali a gaban Pyramid na kasar Masar a tsakanin gidajen rediyo mai hoto na kasashen biyu. Wannan kuma karo na farko ne da gidajen rediyo mai hoto na kasashen biyu za su watsa wannan shagali a lokaci daya a karshen watan Yuni da muke ciki. Bugu da kari kuma, wannan kuma karo na farko ne da shugabannin gwamnatocin kasashen biyu suka halarci irin wannan shagali tare a gaban Pyramid."

Wannan shagali ya kunshi shirye-shirye kimanin 21 ciki har da wasannin kwaikwayo na Peking Opera da wasan acrobatik da nune-nunen salon tufafin gargajiya na kasar Sin da dai sauransu. Madam Hao, 'yar kasar Sin wadda ta riga ta yi zama a kasar Masar har na tsawon shekaru fiye da 10 ta yi farin ciki sosai ta ce, "Na yi zama a kasar Masar har na tsawon shekaru fiye da 10. Ina farin ciki sosai domin shagalin da masu zane-zanen fasahohi na kasar Sin suka kawo mana. A ganina, an ci nasara sosai wajen shirya wannan shagali. Muna fatan zumuncin da ke tsakanin Sin da Masar zai yi zama a duniya har abada."

A cikin 'yan shekarun da suka wuce, kasar Sin da kasar Masar sun yi musayar al'adu sosai. Mutanen kasar Masar wadanda suke koyon harshen Sinanci kuma suke iya harshen Sinanci suna karuwa. Alal misali, a jami'ar Ain al-Shams ta kasar Masar, yawan dalibai wadanda suke koyon harshen Sinanci ya kai fiye da dari 7.

Shirye-shiryen da aka yi a gun shagalin sun kuma jawo hankulan dukkan 'yan kallo. Malam Ahmed Nazif, firayin ministan kasar Masar ya yaba wa zumuncin da ke kasancewa a tsakanin kasar Masar da kasar Sin. Ya ce, "A matsayin zuriyoyin mutane wadanda suka gina Pyramid, muna son nuna fatan alheri da yunkurinmu na tabbatar da zaman lafiya ga zuriyoyin mutane wadanda suka gina Doguwar Ganuwa ta kasar Sin da duk duniya. Muna fatan za mu kara sada zumunta da yin hadin guiwa a tsakaninmu. Mun gode muku kwarai da gaske. Zumuncin da ke tsakanin Sin da Masar yana nan duniya har abada."

Sannan kuma, Mr. Wen Jiabao, firayin ministan kasar Sin wanda ya kuma halarci shagalin nan, ya bayar da wani jawabi, inda ya ce, "Abokanmu, ya kasance da wani karin magana a kasar Masar, wato dauwamammen abu a duniya shi ne lokaci, kuma wanda ya fi lokaci dadewa a duniya shi ne Pyramid. Na amince da cewa, zumuncin da ke tsakanin Sin da kasar Masar kuma ya jure a cikin dogon lokacin da ya wuce zai zauna a nan duniya har abada kamar wayin kai na dan Adam. Lokacin da muke taya murnar cikon shekaru 50 da kafuwar dangantakar diplomasiyya a tsakanin Sin da Masar, bari mu hada da juna domin kara sabbin abubuwa ga zumuncin da ke tsakaninmu." (Sanusi Chen)