Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-26 16:19:50    
Ziyarar da firayin ministan kasar Sin Wen Jiabao ya yi a kasashen Afirka ta sami sakamako da yawa

cri

A ran 25 ga wata, Mr. Wen Jiabao firayin ministan kasar Sin ya dawo gida bayan ya yi ziyara a kasashe 7 na Afirka. A cikin kwanaki 8 da suka wuce, firaminista Wen Jiabao ya yi ziyarar a kasashen Masar, Ghana, Kongo Brazzaville, Angola, Afirka ta kudu, Tanzania da Uganda bi da bi, ya aika da abokantaka ta jama'an kasar Sin ga jama'an kasashen Afirka, kuma ya kawo wa zumuncin da jama'an kasashen Afirka suka nuna wa jama'an kasar Sin. Mr. Huang Shejiao tsohon jakada na kasar Sin da ke kasashen Ruwanda da Kongo Kinshasa ya gana da manema na manema labaru na gidan rediyonmu ya ce, ziyarar da firaministan kasar Sin ya yi a kasashen Afirka ta sami sakamako da yawa.

Mr. Huang Shejiao yana tsamani, ziyarar da Wen Jiabao ya yi wani mataki ne mai muhimmanci da kasar Sin ta dauka a sabon karni don shimfida manufofin da kasar Sin take tafiya kan kasashen Afirka. Ya ce ziyarar ta sami sakamako a fannoni uku.

"Da farko, firaminista Wen Jiabao ya yi shawarwari tare da shugabannin kasashen 7 kan kafa huldar abokantaka bisa manyan tsare tsare ta sabon matsayi. Na biyu kuma, gwamnatin kasar Sin tana mai da hankalinta sosai kan taron koli na dandalin tattaunawar hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen Sin da Afirka da za a yi a watan Nuwamba na shekarar da muke ciki. Mr. Wen Jiabao ya aika da gayyatar da shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya yi wa shugabannin kasashen 7, kuma sun karbi gayyatar cikin farin ciki, sun nuna cewa za su yi kokari don ba da gudummawa. Na uku, An sami nasarori kan batun Taiwan. Kasashen 7 dukansu suna goyon bayan ka'idar 'kasar Sin daya tak a duniya' ".


1  2  3