Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-17 18:01:26    
Sin da Afrika sun shiga sabon lokacin hadin kansu a duk fannoni, in ji kwararren kasar Sin

cri

Shekarar nan ita ce zagayowar shekaru 50 da aka fara kulla huldar diplomasiya a tsakanin Sin da kasashen Afrika. Malam Wang Hongyi, kwararren kasar Sin a fannin harkokin Afrika kuma mataimakin shugaban ofishin nazarin harkokin Afrika na cibiyar nazarin harkokin duniya ta kasar Sin ya bayyana a kan wannan cewa, a cikin shekarun nan 50 da suka wuce, kasar Sin da kasashen Afrika sun taba kai hadin guiwarsu a fannin siyasa da tattalin arziki zuwa wani sabon mataki har sau biyu.

Yanzu kasar Sin da kasashen Afrika sun riga sun shiga cikin wani sabon lokacin hadin guiwarsu daga duk fannoni. Ya ce, "an kai hadin kai tsakanin Sin da kasashen Afrika zuwa wani sabon mataki ne tun daga shekarun 1950 zuwa shekarun 1960, wato lokacin da kasashen Afrika suka tashi tsaye don neman samun 'yancin kansu. A cikin wannan tsawon lokaci, kasar Sin da kasashen Afrika sun hada guiwarsu sosai a fannin siyasa, don neman samun 'yancin kansu da bunkasa harkokin tattalin arzikinsu. Wannan shi ne karo na farko. Bayan da kasar Sin ta fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare da bude wa kasashen waje kofa, ita da kasashen Afrika sun yi ta inganta huldar da ke tsakaninsu a fannin tattalin arziki da ciniki, kuma sun sami babban ci gaba a fannoni daban daban. Wannan shi ne karo na biyu. Haka kuma tun daga faron shekarar nan har zuwa yanzu, kasar Sin ta taba bayar da takardar manufofinta game da harkokin Afrika, Mr Li Zhaoxing, ministan harkokin waje na kasar ya yi ziyara a Afrika, bayan haha Mr Hu Jintao, shugaban kasar Sin shi ma ya yi ziyara a Afrika, ga shi yanzu kuma Mr Wen Jiabao, firayim mininstan kasar yana ziyara a Afrika. Ban da wadannan kuma za a shirya taron koli na dandalin tattaunawa kan hadin guiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika a shekarar nan. Duk wadannan sun alamanta cewa, Sin da kasashen Afrika sun shiga cikin wani sabon lokacin hadin guiwarsu daga duk fannoni. "

An riga an sami kyakkyawan sakamako da a zo a gani wajen yin hadin guiwa a tsakanin Sin da kasashen Afrika daga duk fannoni. Alal misali, jimlar kudi da aka samu daga wajen ciniki a tsakanin Sin da kasashen Afrika ya karu daga dalar Amurka miliyan 12 tun can farko har zuwa kimanin dalar Amurka biliyan 40 a yanzu.

Malam Wang Hongyi yana ganin cewa, dalilin da ya sa an sami sakamako mai kyau kamar haka wajen yin hadin guiwa tsakanin Sin da kasashen Afrika shi ne, domin suna da ra'ayi daya da moriya daya a fannoni da yawa, kuma dukansu suna da burin kara karfin hadin guiwarsu. Ya kara da cewa, "kasashen Afrika da Sin dukanninsu kasashe ne masu tasowa, dukansu sun gamu da kaddara irin daya a zamanin da, haka nan kuma ayyuka da suke fuskanta a yanzu ma irin daya ne, wato kare dinkuwar kasa, da kyautata zaman rayuwar jama'a, da rage gibi da ke tsakaninsu da kasashe masu sukuni. Haka zalika a fannin siyasa, Sin da kasashen Afrika dukansu suna neman kare moriyar kasashe matasa, kuma suna neman tsayawa kan matsayinsu mai adalci a duniya."

Da Malam Wang Hongyi ya tabo magana a kan ziyarar da Mr Wen Jiabao, firayim ministan kasar Sin ke yi yanzu a kasashen Afrika, sai ya ce, "ziyarar da firayim minista Wen Jiabo ke yi a Afrika a lokacin zagayowar shekaru 50 da aka fara kulla huldar diplomasiya a tsakanin Sin da kasashen Afrika, wani babban mataki ne da aka dauka don kara inganta dangantakar aminci ta hadin guiwa a tsakanin Sin da kasashen Afrika. Tabbas ne, ziyarar nan za ta taka muhimmiyar rawa wajen kara karfin hadin guiwa a tsakanin Sin da kasashen Afrika. (Halilu)