Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-25 17:04:20    
Zantutukan da Mr Li Zhaoxing ya yi a kan ziyarar da Mr Wen Jiabao ya yi a kasashe 7 na Afrika

cri
Daga ran 17 zuwa ran 24 ga wannan wata, firayim ministan kasar Sin Wen Jiabao ya yi ziyarar aiki a kasashe 7 na Afrika, wato kasar Masar da Ghana da Kongo Kinshasha da Angola da Afrika ta kudu da Tanzaniya da Uganda. Bayan ziyarar, ministan harkokin waje na kasar Sin Li Zhaoxing wanda ke rufa wa Mr Wen Jiabao baya a gun ziyarar ya bayyana cewa, ziyarar ta cim ma burin kara zurfafa zumunci da kara habaka fannonin yin hadin guiwa da samun bunkauwa gaba daya, wannan tabban ne zai ba da tasiri mai zurfi ga raya huldar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika a cikin sabon zamani.

Bisa bayanin da Mr Li Zhaoxing ya yi, an ce, ziyarar firayim minista Wen Jiabao ta ketare duk fadin nahiyar Afrika, yawan tsawon hanyar ziyara da ya yi ya kai kilomita dubu 35, wato daga gabas zuwa Yamma, sa'anan kuma daga kudu zuwa arewa a shiyyoyi daban daban, karon nan karo ne da shugabannin kasar Sin suka yi ziyara a kasashen Afrika mafi yawa, daga cikinsu da akwai wasu kasashen da firayim ministan kasar Sin yan yi ziyara a karo na farko. Lokain da ya tabo magana a kan tasirin da ziyarar ta yi ga raya huldar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, Mr Li Zhaoxing ya takaita wasu abubuwa cewa,

Da farko, ziyarar ta kara zurfafa zumuncin gargajiya da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika. Mr Li Zhaoxing ya bayyana cewa, babban makasudin ziyarar da Mr Wen Jiabao ya yi shi ne, kara zumuncin da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, jama'ar Afrika su ma sun yi matukar maraba da aminansu na kasar Sin cikin himma da kwazo. Shugabannin Bangarorin biyu dukansu sun bayyana cewa, kodayake da akwai nisa a tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, amma a kodayaushe ana iya jin dankon zumunci da karfi sosai. A duk tsawon lokacin ziyarar, ba sau daya ba ba sau biyu ba firayim minista Wen Jiabao ya kai ziyara a makarantu da yin rangadin aiki a wuraren aiki da kuma yin ma'amala da jama'ar wuraren da ya sa kafa cikin aminci, har ma ya je duddubawar masu kamu da ciwon sida da suke kwantawa a wata cibiyar warkar da ciwace-ciwace, kuma ya ba da kyautar magungunan ciwon zazzabin sauro ga wasu kasashen Afrika tare da rarrabawa dalibansu kayayyakin karatu da isar da fatan alheri da jama'ar kasar Sin suka yi wa 'yanuwan kasashen Afrika.

Na biyu, ziyarar ta cim ma burinta na kara habaka hadin guiwar samun moriyar juna da nasarar gaba daya. Mr Li Zhaoxing ya bayyana cewa, a duk tsawon lokacin ziyarar, Mr Wen Jiabao ya ba da lacca a kasar Afrika ta kudu, inda ya bayyana ra'ayin kasar Sin na raya huldar abokantaka irin ta sabon salo na amincewar juna da yin zaman daidai wa daida da yin hadin guiwar samun nasarar gaba daya da yin ma'amalar juna da yin koyi da juna bisa manyan tsare-tsare a tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika. Bangaren kasar Sin shi ma ya rattaba hannu tare da kasar Masar da Afrika ta kudu a kan tsarin kara zurfafa huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare, sa'anan kuma tare da sauran kasashe 5 ne ta bayar da hadadiyyar sanarwar da ke ba da jagoranci da tsara fasali ga hadin guiwar da ke tsakanin bangarorin biyu bisa manyan tsare-tsare. Bangaren kasar Sin da kasashe 7 sun rattaba hannu kan yarjejeniyoyi da yawansu ya kai 71 wadanda suka shafi siyasa da tattalin arziki da cinikayya da gina manyan ayyuka da al'adu da ba da ilmi da kimiyya da fasaha da sauran fannoni. Ban da hakan kuma, bangaren kasar Sin shi ma ya yi alkawarin ci gaba da samar wa kasashen 7 taimako don raya zamantakewar al'umma , saboda haka ya sami yabo sosai daga wajen kasashe daban daban.

Sa'anan kuma, ziyarar ta sami sakamako na kara amincewar juna da yin watsi da tsakanin da aka shiga da samun fahimtar juna.Mr Wen Jiabao ya bayyana cewa, da sahihanci sosai ne kasar Sin ta mai da hankali ga kasashen Afrika da kuma ba da taimako ga kasashen Afrika, kuma tana son yin hadin kai da hadin guwia da kasashen Afrika bisa tushen girmama wa juna da rashin yin shishigi a cikin harkokin sauran kasashe da yin zaman daidai wa daida da samun moriyar juna. Zantutukan da aka yi na cewar wai kasar Sin ta kawo kalubale ba su dace da hakikanan abubuwan tarihi ba, kuma ba su dace da halin da huldar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika suke ciki ba, ba su dauki nauyin da ke bisa wuyan su ba.(Halima)