Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-20 17:22:03    
Firaministan kasar Sin ya halarci bikin kammala aikin hanya a kasar Ghana

cri

A ran 19 ga wata, tare da shugaba Kufuor na Ghana ne, firaministan kasar Sin, Wen Jiabao, wanda a lokacin ke yin ziyara a kasar Ghana, ya halarci bikin kammala aikin gyara da fadada wata hanyar mota ta Ghana da gwamnatin kasar Sin ta ba da taimako ga wannan aiki. Sabo da haka, yanzu sai ku saurari wani rahoton da wakilanmu suka aiko mana daga bikin.

Wannan hanyar mota da aka kammala ta hada birnin Accra, babban birnin kasar Ghana da kuma birnin Kumasi, wanda ya zo na biyu a wajen girma a arewacin kasar. Wannan hanyar mota dai, tana da muhimmanci sosai a wajen zirga-zirga a tsakanin kudancin kasar da kuma arewacinta, kuma tana da muhimmiyar ma'ana a fannin tattalin arziki. A gun bikin, firaministan kasar Sin, Wen Jiabao ya ce, 'wannan alama ce daban ta hadin gwiwar aminci da ke tsakanin kasashen biyu, haka kuma ta kara karfafa zumuncin gargajiya da ke tsakaninsu.'

An fara aikin gyara da fadada hanyar nan da ke tsakanin Accra da Kusami ne tun daga watan Mayu na shekara ta 2004, kuma gwamnatin kasar Sin ta bayar da rancen kudin da yawansa ya kai kudin Sin yuan miliyan 180 kuma ba tare da sanya kudin ruwa ba ga wannan aiki ba. Domin wannan aiki, rukuni na biyar na babban kamfanin ayyukan hanyoyin dogo na kasar Sin wanda ya dauki nauyin wannan aiki ya zabi ma'aikatan fasaha da na aikin gudanarwa masu kyau, kuma ya sayi na'urori masu inganci, ya tsara shirin aiki sosai.

Game da wannan kyakkyawan aikin da bangaren Sin ya yi, wata jami'ar gwamnatin babban lardin Accra, Madam.Theresa Tagoe ta ce 'A da, wannan hanya kullum cike take da motoci, a lokacin da aka sami cunkuson mota a ranakun Asabar da Lahadi kuma, a kan shafe awoyi uku zuwa hudu, ga yanzu an gyara wannan hanya an magance mana wannan babbar matsala.'

Ba ma kawai wannan sabuwar hanya ta rage yawan lokacin tafiya a tsakanin Accra da Kumasi ba, har ma ta kara lafiya da dadi a wajen tafiya. A sa'i daya kuma, wannan hanya za ta kuma kyautata da bunkasa ciniki da dai sauran masan'anatun da ke gafen hanyar. Shugaban kasar Ghana, Mr. Kufuor ya nuna godiya ga kungiyar aikin gine-gine ta kasar Sin, kuma ya yi fatan za su ci gaba da ba da taimako ga Ghana. Ya ce, 'Ta wannan aiki ne mun ga ingancin aiki na kamfanin ayyukan hanyoyin dogo na kasar Sin, sabo da haka muna matukar fatan za su tsaya su ci gaba da taimaka mana wajen ayyukan gyaran sauran hanyoyi.'

Hasali ma dai, wannan aiki na gyara da fadada hanyar da ke tsakanin biranen Accra da Kusami yana daya daga cikin ayyukan ba da taimako da kasar Sin ta bai wa Ghana kawai ne. A cikin shekaru da dama da suka wuce, bangarorin biyu sun aiwatar da hadin gwiwa mai inganci a fannonin siyasa da tattalin arziki da kiwon lafiya da al'adu da dai sauransu. Firaminista Wen ya ce, 'bisa karfinta ne gwamnatin kasar Sin ta ba da taimako ga Ghana cikin sahihanci da zumunci, kuma ta aiwatar da ayyukan gina gidan wasan kwaikwayo da gyaran hanyoyi da gina sansanonin soja da na 'yan sanda da dai sauransu a kasar. wadannan ayyuka kuma, sun karfafa fahimtar juna da zumunci a tsakanin jama'ar kasashen biyu, haka kuma ta ba da taimako mai kyau ga bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'umma na Ghana.'

A cikin shekaru 50 da suka wuce, yawan ayyukan ba da taimako da kasar Sin ta bai wa kasashen Afirka a wajen bunkasa tattalin arziki da zaman al'umma ya riga ya kai kusan 900. A yayin da gwamnatin kasar Sin ke ba da taimako ga kasashen Afirka ta hanyoyin ba da rancen kudi ba tare da ruwa ba da ba da agaji ba tare da biyan kudi ba da ba da rancen kudi cikin gatanci da dai sauransu, haka kuma ta sa kaimi ga kamfanoni masu karfi na kasar da su je Afirka don zuba jari da aiwatar da hadin gwiwar tattalin arziki da fasaha ta hanyoyi daban daban. Aikin nan na gyara da fadada hanyar da ke tsakanin Accra da Kumasi shi ne aka yi amfani da jari da fasaha na kasar Sin, haka kuma ya rage kudin da aka kashe, ya kuma samar da guraben aiki da kuma horar da kwararru ga kasashen Afirka, ya tabbatar da taimakon juna a fannin da ake kwarewa ke nan.(Lubabatu Lei)