Dangane da sakamakon binciken, madam Zhang Chuji, wata likita da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta yi mana karin bayani da cewa, kara shan hasken rana yana taimaka wa jikin dan Adam bullo da bitamin D. Irin wannan bitamin mai muhimmanci yana amfanawa lafiyar dan Adam daga fannoni daban daban. Alal misali, Bitamin D yana taimakawa wajen daidaita yawan sinadarin Calcium a jikin dan Adam, ta yadda zai kara koshin lafiyar kashi, hakora, da jijiyoyi.
A 'yan shekaru da suka gabata, akwai shaidun masana lafiya da dama da suka nuna cewa, mai yiwuwa bitamin D zai taimakawa wajen yaki da wasu cutututukan da suka dade suna addabar mutane, ciki had da wasu nau'o'in cututtukan sankara. Amma a baya, an gudanar da yawancin irin wannan nazari ne tsakanin Turawa da kuma mutanen da ke zaune a nahiyar Americas. Nazarin da aka gudanar tsakanin 'yan nahiyar Asiya ba su da yawa sam.
Wannan kungiyar nazari ta yi karin bayani da cewa, sun tantance bayanan da aka gudanar a kasar Japan dangane da lafiyar al'umma, wadanda suka hada da mata da maza 33,700, 'yan shekaru 40 zuwa 69 da haihuwa. Wadannan mutane sun gabatar da bayanansu dangane da tarihin jinyar da suka yi, al'adar cin abinci, hanyar zaman rayuwa da dai sauransu, tare da gabatar da jininsu don tabbatar da yawan bitamin D da ke cikin jikinsu.
A cikin shekaru 16 da kungiyar nazarin suka dauka suna gudanar da nazarin, a cikin wadannan mata da maza 33,700, wasu 3301 sun kamu da ciwon sankara. Masu nazarin sun gano cewa, idan ba a yi la'akari da shekarun wadannan mutane ba, ko suna shan taba ko giya ko a'a, matsalar kiba da sauran dalilan da suka kara barazanar kamuwa da ciwon sankara ba, to, samun bitamin D da yawa a cikin jikin dan Adam ya rage barazanar kamuwa da ciwon sankara da kashi 20 cikin dari. Musamman ma a fannin rage barazanar kamuwa da ciwon sankarar hanta. Amma ba a gano alakar hakan da fannin rage barazanar kamuwa da ciwon sankarar huhu da mafitsara ba.
Masu nazarin sun nuna cewa, nazarinsu ya tabbatar da gaskiyar maganar "kila Bitamin D yana taimakawa wajen rage barazanar kamuwa da ciwon sankara" a tsakanin 'yan nahiyar Asiya. Amma a sa'i daya sun gano cewa, idan yawan Bitamin D ya kai wani mataki, to, ba zai kasance alheri ga lafiyar dan Adam ba. Nan gaba za su ci gaba da nazarinsu don tabbatar da yawan Bitamin D mafi dacewa a jikin mutane wajen yin rigakafin kamuwa da ciwon sankara. (Tasallah Yuan)