Masu nazari daga jami'ar Columbia ta kasar Amurka sun dauki shekaru 3 suna gudanar da bincike kan tsoffafi mata fiye da dubu 50 wadanda shekarunsu suka wuce 60 da haihuwa dangane da yadda suke cin abinci da yin barci a rayuwar yau da kullum. Masu nazarin sun kuma kidaya mizanin GI, wato yawan sinadaren Carbohydrate dake cikin abinci da yadda yake shafar yawan Glucose a cikin jini. Mizanin GI yana karuwa, to, ma iya cewa, mutane suna kara cin abubuwa dake kunshe da nisadaran kara kuzari da aka sarrafa su sosai, alal misali, burodi, sukari, ruwan soda mai cike da sukari.
Sakamakon nazarin ya shaida mana cewa, a lokacin da aka fara nazarin, tsoffafi mata da suka fi sha'awar cin abubuwa masu sukari da nisadaran kara kuzari da aka sarrafa su sosai sun fi wadanda ba safai su kan ci irin wannan abinci dake haifar da karancin barci har da kaso 11 cikin 100. Bayan shekaru 3 da kawo karshen nazarin kuma, sabbin tsoffafi mata masu fama da rashin isasshen barci wadanda su kan ci abubuwa masu sukari da nisadaran kara kuzari da aka sarrafa su sosai sun fi takwarorinsu fuskantar matsalar rashin isasshen barci har da kaso 16 cikin 100.
Masu nazarin sun yi bayani da cewa, sakamakon karuwar yawan sukari da ke cikin jinin dan Adam, jikin dan Adam kan samar da sinadarin Insulin, don rage yawan sukari da ke cikin jinin dan Adam, amma raguwar yawan sukarin ta kan sanya jikin dan Adam ya samar da sinadaran Hormone na daban, wadanda suka kawo cikas wajen yin barci yadda ya kamata.
Masu nazarin sun yi nuni da cewa, nazarinsu ya ilmantar da mutane dangane da muhimmancin abinci ga wadanda ba sa samun isasshen barci. Dangane da lamarin, madam Zhang Chuji, wata likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta gaya mana cewa, baya ga tabbatar da daidaiton nauyin jiki, magance matsalar rashin samun isassehn barci, wani dalili na daban ne wajen rage cin abubuwa masu sukari da nisadaran kara kuzari da aka sarrafa su. Haka zalika kuma, cin kayan lambu da 'ya'yan itatuwa da yawa suna kare mata daga matsalar rashin isasshen barci. (Tasallah Yuan)