in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Matan da suka daina al'ada kuma suna da manyan kafafuwa ba sa saurin kamuwa da ciwon magudanar jini a zuciya
2020-10-09 15:37:52 cri

Yanzu haka 'yan mata ba su son manyan kafafuwa, ko kuma kiba. A ganinsu siririnta ya fi kyan gani. Amma wani sabon nazari da aka gudanar a kasar Amurka ya gano cewa, ga mata tsoffafi da suka daina al'ada, manyan kafafuwa suna taimakawa lafiyarsu. Matan da ke babban kugu sun fi takwarorinsu wadanda ke da manyan kafafuwa fuskantar barazanar kamuwa da ciwon magudanar jiki a zuciya.

Masu nazari daga kwalejin nazarin ilmin likitanci na Albert Einstein na kasar Amurka da sauran hukumomin nazari sun kaddamar da rahoton nazarinsu cikin mujjalar ilmin ciwon zuciya ta Turai a kwanan baya, inda suka nuna cewa, sun dauki shekaru fiye da 18 suna bincike kan mata dubu 2 da dari 6 da 83 wadanda suka daina al'ada, a kokarin tantance barazanar kamuwa da ciwon magudanar jini a zuciya da mata masu mabambantan sigar jiki suke fuskanta, wato matan da babban kugu da kuma wadanda ke da manyan kafafuwa. A lokacin da aka fara nazarin, wadannan mata ba su kamu da ciwon magudanar jini a zuciya ba. Kuma sun samu daidaiton mizanin BMI na awon nauyin mutum. Amma bayan da aka kammala nazarin, an gano cewa, wasu 291 daga cikinsu sun kamu da cututtuka masu alaka da wannan batu.

Sakamakon nazarin ya shaida cewa, in an kwatanta su da matan da dake babban kugu, sun fi fuskantar barazanar kamuwa da cututtuka da ke da alaka da wannan batu, har sau biyu. Haka kuma, barazanar kamuwa da irin wadannan cututtuka masu ruwa da tsaki da matan da ke da manyan kafafuwa ya ragu da kaso 40 cikin 100, gwargwadon wadanda bas u da manyan kafafuwa. Masu nazarin sun gano cewa, a cikin matan da aka gudanar da nazarin a kansu, matan da ke manyan kugu maimakon manyan kafafuwa sun fi fuskantar barazanar kamuwa da cututtukan. Irin wannan barazana ta fi ta masu manyan kafafuwansu a maimakon kugu yawa har sau fiye da uku.

Masu nazarin sun yi bayani da cewa, sun gudanar da nazarinsu ne kan matan da suka daina al'ada. Don haka ba su san ko haka lamarin yake cikin maza da kuma mata matasa ba tukuna.

Sun kuma ba da shawarar cewa, duk da cewa, matan da suka daina al'ada suna samun daidaiton mizanin BMI na awon nauyin mutum, kamata ya yi su mai da hankali kan sassan jikinsu dake da kiba. Nan gaba masu nazarin sun shirya yin nazari kan alaka a tsakanin yadda matan da suka daina al'adu suke ci da sha da kuma sassan jikinsu da kiba ke taruwa, a kokarin kimanta tasirin da al'adar ci da sha take yi kan lafiyar mata. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China