Tare da fatan baki dayan ma'aikatan sashen Hausa na CRI suna cikin koshin lafiya a birnin Beijing. Hakika na samu zarafin sauraron shirin ku na 'Sin da Afirka' da kuma 'Gani Ya Kori Ji' a ranekun Talata 11 da Laraba 12 ga watan Oktoba.
Na saurari hirar da malam Saminu Alhassan ya yi da malam Dahiru Muhammad wanda ya zo daga tarayyar Nijeriya cikin shirin 'Sin da Afirka'. Ba shakka, taron karawa juna ilimi kan hakar ma'adinai da malam Dahiru ya halatta a kasar Sin bisa gudunmawar wata kungiya mai zaman kanta ya yi ma'ana sosai bisa la'akari da cewa, Nijeriya tana da dimbin arzikin ma'adinan da ba hako su ba ballantana sarrafa su. Wannan abin takaici ne idan an yi duba ga yadda kasar Nijeriya ke dogaro da cinikin danyan mai wanda farashin sa ya fadi warwas, tare da yin watsi da sauran albarkatun kasa da Allah SWT Ya horewa kasar.
Don haka, ina fatan malam Dahiru zai gabatar da shawarwari masu ma'ana ga hukumomi a Nijeriya dangane da muhimmancin sarrafa arzikin ma'adinan karkashin kasa wajen bunkasa tattalin arzikin kasa. Ko ba komai yin hakan zai taimaka wajen samarwa da kasar ta Nijeriya guraben aiki da kuma karin kudaden musaya da take matukar bukata.
Ban da wannan, na saurari shirin 'Gani Ya Kori Ji' wanda malam Ibrahim Yaya ya zanta da malam Louali Souleymane dan jarida da ya zo daga jamhuriyar Nijar bisa gayyatar kungiyar diflomasiyya tsakanin al'ummomin kasashen Sin da Afirka domin ganin irin ci gaban da kasar Sin ta samu a fannoni da dama. Hakika wannan ziyara tana da muhimmanci ga 'yan jaridu wadanda za su iya amfani da kafofin yada labarai wajen jan hankalin hukumomi domin hada kai da kasar Sin ta fannin bunkasa kiwon lafiya, ba da horo ga jami'an gwamnati ko kwararru, har ma da fannin tsaro.
Ina fatan kasashen Afirka za su ci gaba da hada kai da kasar Sin a matsayin ta na kasa mai son tallafa wa kasashe marasa karfin aljihu musamman daga nahiyar Afirka.
Mai sauraron ku a kullum
Nuraddeen Ibrahim Adam
Shugaban kungiyar
Great Wall CRI Listeners' Club
Kanon Dabo, Nigeria