Barkan ku da warhaka. Ina fata kuna cikin koshin lafiya, ina kuma fata ayyuka suna tafiya kamar yadda ake so.
A karshen shekara ta 2001, lokacin da CRI ta cika shekaru 60 da kafuwa, na samu kai ziyara kasar Sin don bukukuwan da aka yi. Ba zan manta da kyawawan wasanni na nishadi da murna da aka gudanar ba.
A karshen wannan shekara, yayin bukukuwa da za a gudanar na murnar shekaru 75 da kafuwar CRI na san aminanku a ko'ina zasu halarci wannan tarihi da za a kafa domin bukin. Saboda haka, ina neman alfarma daga gareku domin bani damar halartar wannan biki da zaku yi a ranar 3 ga Disamban bana na kafuwar CRI.
A tunanina, zan sake yin rubutu na musamman bisa ga tafiyata ta uku zuwa kasar Sin, da kuma kara wayar da kai domin fahimtar kasar Sin a idanun al'ummar kasata kamar yadda na saba a jaridun Hausa na Arewacin Najeriya yayin da na dawo gida.
A yau, muna sane da yadda mutanen kasashe daban-daban ke ta tururuwa wajen ziyartar kasar Sin domin bunkasa harkokinsu na yau da kullum, saboda haka, wannan wata dama ce da nake so zan yi amfani da ita wajen kara fahimtar da al'umma kyawawan nasarori da zasu iya samu daga kulla alaka da Sin.
Hakika, zan yi murna sosai idan na sake samun wannan dama ta sake kai ziyara kasar Sin domin taya ku murna.
Sai naji daga gareku. A huta lafiya.
Naku,
Salisu Muhammad Dawanau
Abuja, Najeriya