Na saurari shirin 'Sin da Afirka' game da ziyarar hadin gwiwa tsakanin matasan Sin da na Afirka wanda malama Maryam da Saminu Alhassan suka gabatar a ranar Talata 13 ga Satumba, 2016.
Hirar matashi Muhammad Nazif Sani da malama Kande Gao kan dalilin zuwansa wannan ziyara da kuma makasudin taron da suka yi. Sannan da muhimmancin wannan ziyara mai ma'ana da tarin albarka.
Muhammad yayi tsokaci sosai game da ra'ayinsa da kuma tunani ko hasashensa bisa ga irin nasarorin da yake gani za a iya samu nan gaba a sakamakon taron, da ziyara irin wannan. Ya kuma yi bayanin burinsa bayan dawowarsa gida.
A tunani na, irin wannan taron hadin gwiwa na matasa yana da kyau kuma zai iya haifar da muhimman tsari masu nagarta ta yadda za a amfana da juna a tsakanin kasar Sin da na Afirka. Ina fata za a fadada wannan tsari na ziyartar kasashen juna domin gano matsaloli da kuma yadda za a magancesu cikin sauri da nasara.
Wannan shiri ya kayatar da ni ainun. Lallai malama Maryam tana kokari wajen jagorantar shirin Sin da Afirka.
Ku huta lafiya.
Salisu Muhammad Dawanau
Abuja, Najeriya