Zuwa ga Malama Fatima Liu CRI Hausa, Bayan dubun gaisuwa dafatan dukkanin ma'aikatan sashin Hausa suna cikin koshin lafiya a birnin Beijin kamar yadda nake a birnin Kanon Dabo lafiya.
Bayan haka na karanto rahota da kuka gabatar akan lokacin bazara a lardin Tibet na kasar Sin, lallai naji dadin wannan rahota da kuma samun sha'awar wannan guri musammam mutanen gurin, al'adunsu, zamantakewarsu da rayuwarsu tayau da kullum musammam a cikin wannan lokaci na bazara. Gaskiya kasar Sin kasace mai dumbin al'umma, al'adu masu dadi da kyau dasan baki da karramasu. Bayan haka rahoto da kuka gabatar akan yadda kasar Sin take taimakawa kasashen Afirka da bangaren tsaro yayi dadai muma mun shaida sannan mun yadda ganin takanar takano suke turo dakarun kasashe daban daban a lokaci-lokaci, banda kayan aiki da suke bayarwa. A gaskiya mu'amula tsakanin kasar Sin da Afirka tana samun bunkasuwa. Nagode.
Wassalam, Abdulkadir Ibrahim, G.C.L.C Kano.