in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Allah Daya Gari Bambam ya kayatar da mu masu sauraro
2016-02-14 12:30:21 cri

A gaskiya yadda malama Lubabatu da Malam Mamman Ada suka gabatar mana da shirin Allah Daya Gari Bambam a ranar juma'a 05 ga watan February, 2016 ya kayatar da mu masu sauraro yadda yakamata kuma tsokacin da malaman suka yi a cikin shirin ya kara mana wayin kai bisa tarishi da kuma irin shagulgulan bikin sabuwar shekarar bazara ta al'adun gargajiya na kasar Sin. Babu shakka wannan bikin sabuwar shekarar bazara ta kasar Sin ta burgeni sosai ganin yadda sinawa ke karrama bikin ta hanyar shagulgula da liyafa iri-iri inda sinawa kan taru a gidan iyali su ci abunci tare da junansu kuma su taya junansu murna kuma su shirya liyafar masamman ta murnar shigowar sabuwar shekarar bazara tare da shirya liyafar ban kwana da tsohuwar shekarar bazara. Amma dai, na yi matukar yin mamakin jin cewa, tarishin bikin shekarar bazara ya kai shekaru 4000, wato an fara bikin bazara a kasar Sin kimanin shekaru 4000 da suka gabata. Muna taya jama'ar kasar Sin masamman ma ma'aikatan sashin Hausa na Radiyo kasar Sin da fatan za ku kammala bukukuwa da shagulgula lafiya kalau, amin.

Daga Alhaji Ali kiraji Gashua.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China