Yanzu muna maida hankali bisa ziyarar da mr. Wang Yi firaministan kasar Sin zai fara yi a kasashenmu na Afirka su 4. Wannan ziyarar, wani muhimmin mataki ne da kasar Sin ta dauka dan kara kyautatuwar huldar diplomasiya da musayar al'adu da kara hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare bisa sabbin matakan samun bunkasuwa a tsakanin sabuwar Sin ta zamani da kasashen Mizambiq, Mautrius, Zambia da kasar Malawi. Muna fata mr. Wang tare da tawagarsa za su yi ziyara a cikin nasara kuma su daddale muhimman shawarwari da rittaba hannu bisa muhimman aiyukan raya kasa a tsakaninsu. Kana wannan ziyara ta mr. Wang Yi a nahiyarmu ta Afirka ya kara alamunta amunci dake akwai tsakanin kasar Sin da ma daukacin kasashenmu na Afirka.
Daga Alhaji Ali kiraji Gashua.