in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Muna bukatar kasar Sin a Nigeria
2016-01-25 13:43:20 cri

Kasar Sin da taraiyar Nigeria suna da kyakkyawar huldar abokantaka da kuma huldar diplomasiyya mai kyau kuma mahukuntan kasashen 2 na ci gaba da kara bunkasa dankon zumuncin dake a tsakaninsu bisa matakan diplomasiyya bisa kawaici da martaba juna a dogon lokaci idan aka yi la'akari da yadda kasar Sin da Nigeria ke kara samun ci gaba bisa yin mu'amula da juna bisa sabbin matakan samun bunkasuwar tattalin arziki ta fannin hadin gwiwa da kara zuba jari bisa manyan tsare-tsare. Shugabannin kasar Sin sun bada muhimmiyar gudumowa ta fannin bunkasa hadin gwiwa da samar da zaman karko a dud duniya kana sin na kara bada muhimmiyar kulawa da kuma taimako ga kasashenmu na Afirka masu tasowa.

A shekarar bara wato 2015, kasar Sin sun bada muhimmiyar gudumowa da kuma taimako mai yawa ga kasashenmu na yammacin Afirka wayanda suka yi fama da cutar Ibola. Dan haka ne ma, muke ganin ya kyautu nahiyar Sin da Afirka su ci gaba da yin hulda da juna dan samar wa al'ummomin kasashensu katuwar moriya bisa karko. A shekarar 2015 ne, a taraiyar Nigeria mu samu sabuwar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da muka zaba, kuma burin gwamnatin Muhammadu Buhari shine su murkushe aiyukan cin amanar kasa wato cin hanci da kuma nuna halin ba shina ba sabo ga duk wanda aka kama da laifukan cin amanar kasa. To, yanzu mahukuntan kasar Sin sun yi kaurin suna sosai wajen yin kokuwa da kuma yaki da cin amanar kasa da suka hada da cin hanci da karbar rashawa da sauran manyan laifuka dake yin illa ga tattalin arzikin kasarmu Nigeria a dogon lokaci.

Muna fata gwamnatin kasar Sin za su ba wa gwamnatin shugaban kasarmu Nigeria hadin kai bisa bada shawara ta yadda saban shirin yaki da cin hanci a kasarmu Nigeria zai kai ga samun babbar nasara ganin yadda kasar Sin ke nuna halin dagewa ga yaki da cin hanci da karbar rashawa da sauran laifuffukan cin amanar kasa wanda kuma dud duniya mun shaida manyan nasarorin da gwamnatin kasar Sin ta jks karkashin jagorancin shugaban kasar Sin mr. Xi Jinping suka samua yaki da cin hanci .

Daga Alh. Ali kiraji Gashua.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China