Ina fata kuna cikin koshin lafiya.
Kwana biyu bamu yi mu'amala ba shi yasa naga zai dace in aika muku sakon gaisuwa da fatan alheri, sannan in kuma sanar da ku cewar 'ina tare da ku a kullum'.
Bugu da kari, zan ci gaba da baku shawarwari da kuma yin tsokaci game da nagartattun shirye-shiryenku a duk lokacin da ya dace.
Ina so ku sani cewar, a kullum kuna fadakarwa, sannan kuna kara fahimtar da mu masu sauraren ku a fadin duniya. A nan ina iya cewa, ina karuwa matuka da shirye-shiryenku, haka kuma na tabbata miliyoyin masu sauraren ku na fadin duniya suma sun samu karuwa da fahimta mai tarin yawa da taimakon ku a sashen Hausa. Tun da abin haka yake, to muna iya cewa, 'jinjina da gaisuwa ta musannan zuwa gare ku', allah Ya baku ladan aiki, Ya kuma kara muku basira.
Bayan wannan, koda yake na san komai yana tafiya ne bisa tsari, amma dai masu sauraren ku da dama suna ta yin korafi cewar 'yanzu baku shirya musu gasar kacici-kacici' kamar yadda kukan yi a can baya.
A gani na, wannan korafi ne mai bukatar amsa daga gare ku, koda kuwa ta shirin 'Amsoshin Tambayoyin ku' ne domin masu sauraren ku su fahimta.
A takaice, ina iya cewa, kuna bayar da himma sosai fiye da baya. Na jinjina muku sosai. Allah Ya taimaka.
Naku a akullum,
Salisu Muhammad Dawanau,
Abuja, Najeriya