in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sako daga malama Rabiatou Abarchi daga birnin yamai, Nijer
2016-01-24 13:20:24 cri
Bayan gaisuwa da fatan alkairi a cikin wannan sabuwar shekarar 2016 a tuntuni muke a ciki, a cikin rahoton mu na farko a cikin wannan shekarar 2016, na dauko ne da ra'ayoyin masu saurare a garin Maradi ta jamhuriyar Nijer. Na samo ra'ayoyinsu ne ta hanyar wata ziyara da na kai a can, nan ne na ci karo da wasu daga cikin masu sauraren sashen hausa na CRI wadanda kuma suka yarda su bayyana mini ra'ayinsu a kan shirye-shiryenku na kullum.

Hakikanin gaskiya a lokacin da na bayyana kaina a matsayin mai dauko ra'ayoyin masu sauraren CRI a yamai ga matasan da suka halarci wani taro da muka gudanar dasu domin mun je Maradi ne wani taron mahawarar da ya tattara matasa fiye da 150 anan ne na samu damar tattaunawa dasu shirye-shiryenku kuma sun nuna farin cikinsu sosai da damar da zasu samu don bayyana ra'ayoyin a kan yadda suke jin shirye-shiryenku tare kuma da bayyana wasu bukatocinsu ga CRI, har ila yau kuma da mika goyon bayansu ga duk daukacin ma'aikatanku.

Shirye-shiryen da matasan suka fi maida hankali a kan su dai sune Shirin SIN da AFIRKA da kuma TASKAR SINAWA da kuma jagoran duk wasu shirye-shiryenku wato shirin ALLAH DAYA GARI BANBAN.

SIN DA AFIRKA a nan lalle matasan maradi sun nuna cewa shirin na matukar burgesu don damar da kuke ba yan Afirka musaman na Nijer da Najeriya tofa albarkacin bakinsu a kan yadda suka ga TSARIN kasar SIN da kuma dalilin zuwansu a CANA. Baya ga wannan, matasan sun bukaci cewa in da hali CRI ta rinka shirya wata kwanbala da zata ba masu saurare damar cinyewa sai ku yi musu tukuyci da VISA ta zuwa kasar SIN don yin ziyara a SIN wannan shi ne burin matasan garin MARADI.

TASKAR AL'ADUN SINAWA wannan shirin ma matasan garin Maradi sun bayyana jin dadinsu garesa domin sun ce ta hanyar wannan shirin taskar sinawa sun samu sanin dumbin al'adun da kasar SIN ta kumsa wanda a ganinsu shi yake kara basu kwarin gwiwa da kuma sha'awar zuwa kasar ta SIN.

sai shiri mai farin jinni shirin ALLAH DAYA GARI BAMBAN anan jinjina da yabo ne masu saurare a garin Maradi suka fara da shi ga magabatan sashen hausa na CRI da suka fito da wannan hazakar ta gabatarma masu saurare da wannan shirin na Allah daya gari Banban wanda ke ci gaba da taka rawar azo a gani a jamhuriyar Nijer musaman a garin Yamai da Maradi, a farko idan aka yi mini tambayar shin ko za'a iya samun wata jaha a Nijer da aka fi sha'awar shirye-shiryen rediyon CRI fiye da yamai to wallahi zan ce babu kamar yamai to amma sai na ga akasin haka a garin Maradi don a can kusan ma masu sauraren cri sun lunka masu saurare a yamai.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China