Wannan taro na kasashen Sin da Afirka mai suna FOCAC da zai gudana a kasar Sin Afirka, muna fatan cimma manyan nasarori masu yawan gaske. Karin hasken da ministan harkokin wajen kasar Sin mr. Wang Yi, ya yi wa manema labaru a ranar alhamis din makon jiya, ya alamunta damuwar da kasar Sin take da shi na samar da moriya ga kasashenmu na Afirka masu tasowa, ganin mr. Wang Yi ya nuna cewa, kasar Sin zata samar da wasu tsare-tsaren hadin gwiwa mai kyau tsakaninta da aminanta Kasashenmu na Afirka inda taron zai maida hankali ga batun masana'antu da koyawa kasashenmu na Afirka dabarun noma na zamani da kuma magance fatara da talauci da dai sauransu. Muna fatan alheri mai yawa ga kasar Sin da kasashenmu na Afirka a taron FOCAC a kasar Afirka ta kudu. Banda wannan, muna fata sashin Hausa na Radiyon kasar Sin cri za ku maida hankali sosai ga samar mana da labaru da rahotanni masu dumi-dumi a lokacin taron Dandalin FOCAC.
Daga Alhaji Ali kiraji Gashua.