A ranar laraba 25 ga watan Nuwamba, 2015 da yammaci, na samu zarafin sauraron shirin Gani Ya kori wanda malamai Mamman Ada, Samunu Alhassan Usman suka samu zarafin gabatar mana. Na gamsu da tsokacin malamai a cikin shirin, inda suka yi bayani adangane da za a magance matsalar da dumamar yanayi ke haifar wa duniyar Dan Adam a cikin dogon lokaci kana tsokacin malaman ya taba batutuwan yadda za a magance matsalar dumamar yanayi da kuma yadda taron kasa da kasa kan dumamar yanayi zai gudana a kasar France. To, amma a nawa ra'ayin adangane da taron kasashen duniya a birnin Paris na kasar Faransa kan dumamar yanayi, yana da kyau manyan kasashen duniya masu arzikin mana'antu da su himmatuwa sosai tare da sa kaimi bisa dogon nazari bisa yadda za a lalibo hanyoyin samun sauki daga illolin da dumamar yanayi ke haifar wa duniya kana mahalarta taron birnin Paris su kara sa himma bisa fito da wasu tsare-tsare na masamman a kasashensu ta yadda za su samu zarafin murkushe matsalar dumamar yanayi tun daga tushe kuma a cikin hanzari. Banda wannan, a kasarmu taraiyar Nigeria gurbacewar yanayin duniya na shafar harkokin aikin gona inda a duk shekara muke fuskantar matsalar karancin ruwan sama, damuna bata sauka da wuri, amma kuma damunar tana karewa da wuri. Wannan matsala tana haifar da muguwar matsala sosai ga harkokin noma a taraiyar Nigeria, masamman yankin arewacin Nigeria inda matsalar ta yi kamari sosai. Muna fata taron kasa da kasa da zai gudana a birnin Paris na kasar Faransa zai cimma matsaya mai kyau bisa yadda za a magance matsalar gurbacewar yanayin duniya cikin hanzari, amin.
Daga Alhaji Ali kiraji Gashua.