A cikin tsawon lokaci, kasar Sin da kayayyakin da aka kera a kasar suna taka muhimmiyar rawa wajen samar da inganci da rahusa a fadin duniya, musamman ma a nan Nahiyarmu ta Afirka. Kuma a hakikanin gaskiya, muna amfana da kayayyakin kasar Sin din.
A can baya, wasu kayayyaki da na'urori masu amfani DA wutar lantarki, sai dai mu kalla a talbijin ko mujallun kasashen waje saboda tsadarsu, amma da taimakon kamfanonin kasar Sin, yanzu muke sarrafa wadannan na'urori da kayayyaki. Idan kuwa aka yi maganar tufafi ko takalma ko wayoyin hannu, to fa sai dai mu 'yan Afirka mu rika godiya ga kasar Sin saboda gudunmuwar da ta bayar da kuma girman tasirin da abin ya haifar.
A sakamakon dokar 'bude kofa ga kasashen waje' da aka zartar a hukumance a kasar Sin, zan iya cewa, an samu rattaba hannu a kan kawawan yarjeniyoyi tsakanin kasar Sin da kasashenmu na Afirka ta yadda ake ta cin moriyar juna. Wannan abin alfahari ne ainun.
Galibin kasashenmu na Afirka suna amfana da kaya kirar kasar Sin, misali; allurai, reza, cokala, kwanukan girki da na cin abinci, flasks, gilasai,fitilu, tocila, kofuna, kyauren kofa da tagogi, kayayyakin wasanni na yara, kayayyakin gini da dai sauransu masu dumbin yawa.
Kafin wannan lokaci, masana da dama sun yi tsokaci da rubuce-rubuce kan tasiri da alfanun dake tartare da kayayyakin kasar Sin a Nahiyarmu, saboda haka, Ina iya cewa, akwai alfanu sosai wajen yin amfani DA layayyakin kasar Sin domin kayayyakin sun taba rayuwata da na al'umma mai yawa ta hanyoyi masu yawa.
Salisu Muhammad Dawanau,
Abuja, Najeriya