in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Alayyaho na iya kara karfin jijiyoyin dan Adam
2015-11-08 10:24:04 cri


Tashar internet ta One News Page ta labarta a kwanan baya cewa, cin alayyaho na taimakawa sosai wajen kara karfin jijiyoyin da ke jikin dan Adam. Saboda akwai abubuwan sinadarin Nitrate masu tarin yawa a cikin alayyaho, wadanda ke taimakawa jijiyoyin da ke jikin dan Adam.

Masu ilmin kimiyya sun gudanar da wani bincike kan beraye, inda suke ba su alayyaho a matsayin abinci a ko wace rana. Sun gano cewa, sinadarin Nitrate masu yawa da ke cikin alayyahon suna kara karfin karuwar furotin iri guda 2 masu muhimmanci wajen gina jijiyoyin da ke jikin dan Adam.

Baya ga alayyaho kuma, ana iya samun dimbin sinadarin Nitrate a cikin kayayyakin lambu wato nau'o'in ganyaye daban daban, kamar latas da ganye mai samar da nau'in sinadarin sukari.

Masu nazari daga kwalejin Karolinska na kasar Sweden sun yi nuni da cewa, yanzu babu wani nau'in abinci ko abin sha mai dauke da sinadarin Nitrate da ke gina jiki da ake sayarwa a kasuwa. Amma abin farin ciki a gare mu shi ne ba mu bukatar cin alayyaho da yawa, da zummar kara karfin jijiyoyinmu. Masu ilmin kimiyya sun baiwa berayen alayyaho kadan ne a ko wace rana.

Masu nazarin sun bayyana cewa, binciken da suka gudanar yana da ban sha'awa ainun a fannin nazarin abubuwa masu gina jiki. Yawan sinadarin Nitrate da ake bukata wajen kara karfin jijiyoyin beraye ba shi da yawa. Amma a bangaren mu 'yan Adam, idan muna son samun isasshen sinadarin Nitrate domin kara karfin jijiyoyinmu, to, akwai bukatar mu kara cin abincin da ke dauke da irin wadannan sinadare. Masu nazarin sun yi fatan cewa, sakamakon nazarinsu zai taimaka wajen lalubo bakin zaren warkar da masu fama da rashin karfin jijiyoyin da ke jikin dan-Adam. Sai dai jama'a na fatan masu nazarin za su ci gaba da binciken nasu ko da bayan samun wannan sakamako, a kokarin kubutad da mutanen da suke fama da lalurar rashin karfin jijiyoyi sakamakon kamuwa da wasu cututtuka ko kuma tsufa.

Wasu nazarce-nazarce da aka yi a baya sun nuna cewa, cin alayyaho na iya rudar mutane, su ji kamar sun koshi. Haka kuma sakamakon wasu nazarce-nazarce sun shaida cewa, cin alayyaho kan taimaka wajen hanzarta warkar da lalurar ciwon zuciya. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China