lafiya1527.m4a
|
Bayanai sun nuna cewa, kukan da jarirai ke yi da zarar an haihuwa su yakan faranta ran iyalai. Domin ana ganin cewa, jariran da suka yi kuka da karfi wai alame ce suna da karfin jiki. Amma wani sabon nazari da aka yi a kasar Japan ya shaida cewa, kukan da jarirai ke yi da zarar an haife su, ba abu ne mai kyau ba. Gwargwadon tsawon lokacin da aka haifi jariri gwargwadon irin kukan da zai yi. Watalika dalilin da ya sa haka shi ne domin jijiyoyin da suka taso daga kwakwalwarsa ta rats makwogoro zuwa kirjinsa ba su kosa ba tukuna.
Masu nazari karkashin shugabancin shehun malama madam Myowa Yamako daga jami'ar Kyoto ta kasar Japan sun tattara kukan jarirai 64 wadanda ke da yunwa, suka kuma tantance kukansu a tsanake. Wadannan jarirai sun hada da jariran da aka haife su ba tare da wani lokaci ba, wadanda suka dauki tsawon lokacin da bai kai makonni 32 ba a cikin mahaifansu, da wadanda wuce makonni 32, amma ba su kai 36 ba, da kuma jariran da aka haife su daidai lokacin da aka yi hasashe, wato tsakanin makonni 37 zuwa 42.
Masu nazarin sun gano cewa, ma'aunin saurin kukan jariran da aka haifa wadanda ba su wuce makonni 32 a ciki ba, ya kaiwa MHz(megahertz) 460 zuwa 642. Ma'aunin saurin kukan jariran da aka haifa wuri, wadanda suka wuce makonni 32 a ciki, amma bai kai 36 ba, yana tsakanin MHz 435 zuwa 609. Sa'an nan ma'aunin kukan da yak e daidai na jariran da aka haife su daidai lokacin da aka yi hasashe yana tsakanin MHz 361 zuwa 524. Lamarin ya shaida cewa, gwargwadon yadda aka haifi jariri da wuri, gwargwadon kuka da karfi da zai yi. Duk da haka masu nazarin ba su gano alakar da ke tsakanin karfin kukan jarirai da kuma nauyin jikinsu ba.
Sakamakon nazarce-nazarce da aka gudanar a baya ya nuna mana cewa, jijiyoyin jariran da aka haida wadanda suka taso daga kwakwalwa suka ratsa ta makogwaro zuwa kirjinsa ba su fara aiki yadda ya kamata ba. Ana ganin cewa, wadannan jijiyoyin suna taka rawa wajen rage ciwon da ake fama da shi a makogwaro. Kukan da jarirai suka yi da karfi yana da nasaba da ciwon da suka ji a makogwaronsu.
Madam Myowa Yamako ta ce, kukan da jarirai ke yi da zarar an haife su, wata alama ce da ke nuna cewa, wadannan jijiyoyin ba su kosa ba tukuna, saboda ba su fara aiki yadda ya kamata ba. (Tasallah Yuan)