in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ciwon karancin basira na Alzheimer's disease yana da nasaba da ciwon tabuwan hankali
2015-09-08 17:07:43 cri

Wani sabon nazari da aka gudanar a kasar Birtaniya ya shaida mana cewa, an samu barkewar cutar raguwar kaifin basira na Alzheimer da kuma gushewar hankali ko tunani a bangaren kwakwalwar mutum, lamarin da ke nuna cewa, akwai alaka a tsakanin wadannan cututtuka 2, hakan zai taimaka wajen gano yadda mutane ke gamuwa da wannan matsala.

Cutar raguwar kaifin basira ko "Alzheimer", wata matsala da ke shafar wani sashe na kwakwalwa da ke da nasaba da tunani. Kana cutar gushewar hankali wata matsala ce da ke sanya kwakwalwar mutum ba ta yi aiki yadda ya kamata. Har yanzu masana kimiya ba su san ainihin dalilin da ke haddasa wadannan cututtuka 2, da kuma yadda cututtukan suke kama mutane ba. Wasu masu nazari na ganin cewa, ko da yake alamun cututtukan 2 kusan ba iri daya ba ne, amma ga alama akwai wata alaka a tsakaninsu.

Masu nazari daga jami'ar Oxford ta Birtaniya da sauran hukumomin nazari sun kaddamar da wani rahoto a jaridar kwalejin nazarin kimiyyar kasar Amurka wato PNAS cewa, sun yi bincike a kwakwalwar mutane 484 ta hanyar amfani da wasu na'urori, wadanda shekarunsu suka wuce 8 a duniya, amma ba su kai 85 ba. Sakamakon binciken ya nuna cewa, an samu irin wadannan cututtuka biyu a cikin kwakwalwarsu.

Aikin sassan kwakwalwar mutum dai shi ne daidaita bayanai, alal misali, daidaita bayanan da aka ji da wadanda aka gani a lokaci guda. Masu nazarin na ganin cewa, sakamakon binciken kwakwalwar mutum ta hanyar amfani da wasu na'urorin da ke amfani da maganadisu ya yi hasashen cewa, mai yiwuwa ne wasu daga cikin sassa kwakwalar wadannan mutanen ba su girma yadda ya kamata ba,don haka za su fuskanci babbar barazanar kamuwa da irin wadannan cututtuka na gushewar tunani ba.

Masu nazarin sun ci gaba da cewa, nan gaba akwai bukatar ci gaba da gudanar da wani babban nazarin musamman na daban kan wannan sakamakon nazari, kana kuma akwai sauran rina a kaba wajen yin amfani da sakamakon nazarin ta fuskar tabbatar da ko mutum ya kamu da cututtukan 2 ko a'a. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China