in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mai yiwuwa ne kamuwa da gyambon cikin kunne sau da dama ya iya haifarwa kananan yara illa wajen bambanta amon murya
2015-10-11 12:11:18 cri

Wani sabon nazari da aka gudanar a kasar Finland, ya nuna cewa idan kananan yara su na yawan kamuwa da cutar gaggawa ta gyambon cikin kunne, mai yiwuwa ne hakan ya haifar musu da illa ga kwakwalwarsu, ta fuskar daidaita harsuna yadda ya kamata.

Masu nazari daga jami'ar Turku ta kasar Finland, da sauran hukumomin nazari sun gabatar da rahotonsu kan mujallar "kunne da yadda mutane suke sauraro", inda suka yi bayanin cewa, sun yi nazari kan kananan yara 20 da shekarunsu suka kai 2 a duniya, wadanda aka taba yi musu tiyata kan dodon kunnensu, saboda kamuwa da cutar gaggawa ta gyambon cikin kunne sau da dama, sun kuma kwatanta su da sauran kananan yara 19 da suka taba kamuwa da cutar gaggawa ta gyambon cikin kunne sau daya ko kuma sau biyu kacal. Dukkan wadannan kananan yara 39 sun yi girma yadda ya kamata, kuma a cikin iyalansu magabata, babu wanda ya taba kamuwa da wata matsala wajen yin magana. Masu binciken sun kuma rubuta yadda kwakwalwarsu ke aiki, yayin da suka saurari harshen Finland.

Tantancewar da suka yi ya shaida cewa, ko da yake ciwon gyambon cikin kunne da a kan sake kamuwa da shi bai kawo wa kananan yaran illa wajen saurara abubuwa ba, amma ga alama ya haifar musu da wata matsala yayin da suke bambance wasu kalmomi. Masu nazarin sun yi bayani da cewa, kananan yara da suka taba kamuwa da ciwon gyambon cikin kunne da a kan sake kamuwa da shi, sun fi maida hankali kan sauye-sauyen karin harshe da karfin murya. Amma ba sa iya nuna kwarewa wajen banbance wasu babbaku.

Masu nazarin sun yi nuni da cewa, a baya masu nazarin kimiyya ba su gudanar da nazari kan wannan fanni ba. Don haka sakamakon nazarinsu zai taimaka, wajen kara sanin abubuwan da su kan kawo illa ga kananan yara yayin da suke koyon yin magana, ta yadda za a ba da taimako wajen kare kananan yara daga gamuwa da matsalar yin magana yadda ya kamata. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China