lafiya1529.m4a
|
Cibiyar nazarin ciwon sankara ta kasa da kasa, karkashin shugabancin hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO, ta fidda sakamakon wani sabon nazari a kwanan baya, wanda ke nuni da cewa idan nauyin jikin mutum ya wuce misali, ko kuma yana kan sahun masu kiba, hakan mummunar alama ce, dake nuna yiwuwar kamuwar sa da ciwon sankara.
Binciken ya nuna cewa a cikin sabbin masu fama da ciwon sankara dake dukkanin sassan duniya a ko wace shekara, kusan mutane dubu 500 sun kamu da ciwon ne saboda nauyin jikinsu ya wuce misali, ko kuma suna kan sahun masu kiba.
Masu nazarin sun wallafa rahoton na su ne kan mujallar "the Lancet" ta kasar Birtaniya, inda suka nuna cewa sun tantance mizanin BMI na mutanen kasashen duniya da dama, kuma bayanan da suka shafi kamuwa da ciwon sankara, da na mutuwa daga shekarar 2002 har zuwa yanzu, sun nuna cewa, a cikin sabbin masu fama da ciwon sankara baligai a shekarar 2012, mutane kimanin dubu 481 sun kamu da ciwon ne saboda nauyin jikinsu ya wuce misali, ko kuma suna kan sahun masu kiba, adadin da ya kai kashi 3.6 cikin dari bisa jimillar sabbin masu fama da ciwon a dukkanin duniya. A cikinsu kuma wasu dubu 393 sun fito ne daga kasashe masu sukuni.
Mizanin BMI, mizani ne na awon nauyin mutum a kilogiram, idan an raba da tsayin mutum a mita sikwaya. Idan ya wuce 25, to, nauyin jikin mutum ya wuce misali, yayin da idan ya wuce 30, mutumin yana kan sahun masu kiba.
A cewar rahoton, abu ne mai sauki wadanda nauyin jikinsu ya wuce misali, ko kuma suke kan sahun masu kiba su kamu da ciwon sankara a makoshi, ko uwar hanji, ko koda, ko a saifa, ko a madaciya. Mata kuwa su kan kamu da ciwon sankara a mama bayan da al'adarsu ta kare, a bangaren kwan mace da mahaifa.
Sakamakon nazarin ya shaida cewa, an fi samun masu fama da ciwon sankara a kasashe masu sukuni, wadanda suka kamu da ciwon sakamakon matsalar kiba, musamman ma a arewacin Amurka. Har wa yau kuma, adadin ya nuna cewa, yawan matan da suke kamuwa da ciwon sankara sakamakon matsalar kiba ya fi na maza yawa.
Rahoton ya bayyana cewa, tun bayan shekarar 1980 ya zuwa yanzu, yawan wadanda suke kan sahun masu kiba ya ninka sau daya a duk fadin duniyarmu. A cikin adadin kuma, galiban wadanda shekarunsu suka wuce 20 a duniya, kashi 35 cikin dari ne nauyin jikinsu ya wuce misali.
Masana sun yi kashedi da cewa, wajibi ne a kiyaye maidaidaicin nauyin jiki, a kokarin rage barazanar kamuwa da ciwon na sankara. (Tasallah Yuan)