Ina fata kuna lafiya.
Masu iya magana kan ce, 'yabon gwani, ya zama dole'. Ko tantama bai kamata a yi ba idan aka ce kun taka muhimmiyar rawa wajen ilmantarwa da fadakarwa, haka kuma a bangaren tunatarwa domin kara wa rayuwa armashi.
A cikin tsawon lokaci, na zanta da mutane masu yawa wadanda galibi suka nuna yabo ta musamman bisa kokarin ku a fagen zakulo bayanai masu nagarta bayan kun tace su kafin ku watsa su ga duniya don kowa ya fahiimta.
A gani na, ko yanzu 'kwalliya ta biya kudin sabulu' idan muka yi la'akari da yanayin shirye-shiryenku na can baya, da yadda abin yake a yau. Sannan kuma sabbin hanyoyi na zamani. suna taka rawa sosai a tsarin ku na yau wadda hakan kan taimaka ainun.
Saura da me? Yanzu sai dai ku ci gaba da bada himma da kwazo da yin aiki tukuru domi 'hakar ku ta cimma ruwa'. Mu kuma zamu ci gaba da ba ku shawarwari daidai yadda ya kamata domin 'a gudu tare, a tsira tare'.
A madadi na, da na wasu masu sauraron ku, ina yi muku fatan alheri, da addu'ar Allah Ya kara taimakawa.
Naku a kullum,
Salisu Muhammad Dawanau