lafiya1519.m4a
|
Masu sauraro, yanzu an shiga lokacin zafe a nan birnin Beijing ya shiga lokacin zafi. Yaya lamarin ya ke a Nijeriya? Sanin kowa ne cewa, a lokacin zafi, jama'a na sha'awar shan mabambantan kankana da danginta da sauran 'ya'yan itatuwa. A sa'i daya kuma, a duk fadin duniya a ko wace shekara wasu su kan kamu da cututtuka sakamakon shan kankana da sauran nau'o'in'ya'yan itatuwa.
Kwanan baya, masana daga kasar Jamus sun yi gargadin cewa, wajibi ne a hanzarta shanye kankana da sauran 'ya'yan itatuwa da zarar an yanka su don gudun ka da kwayoyin cuta su hau kansu .
Andreas Hensel, shugaban cibiyar nazari da kimanta barazana ta kasar Jamus ya bayyana cewa, kwayoyin cutar Salmonella, kwayoyin cutar Listeria, da wani nau'in kwayoyin cutar da ke cikin hanji wadanda ke haddasa zubar jini a cikin hanji, dukkansu su kan sauka a kan naman kankana da danginta marasa tsami cikin sauri. Don ganin an magance wannan matsala da kwayoyin cuta ke hawa kan naman kankana da sauran 'ya'yan itatuwa, kamata ya yi nan da nan jama'a su shanye kankana da danginta da aka yanka su, ko kuma a sanya su a cikin firji.
Mista Andreas Hensel ya kara da cewa, akwai yiwuwar kwayoyin cuta su shiga cikin kankana da danginta da sauran 'ya'yan itatuwa yayin da ake sarrafa su, ko jigilar su, ko kuma adana su. Sa'an nan kuma yayin da mutane suka yanka su a wuri mai kazanta. Har wa yau kuma idan hannun mutum ko kuma kayayyakin dafa abinci ba su da tsabta to wannan datti ko kazanta na iya shiga cikin 'ya'yan itatuwan, saboda haka ya zama dole a rika tsafta ce hannaye da kuma kayayyakin dafa abinci yayin da ake yanka kankana da danginta.
Wannan masani na kasar Jamus ya ci gaba da cewa, idan ba a shanye dukkan kankana da danginta da aka yanke ba, to, tilas ne a rufe sauran yadda ya kamata, daga baya a sanya su cikin firji. Haka zalika, wajibi ne wadanda jikinsu ba zai iya jure kwayoyin cuta ba, kamar tsoffafi, kananan yara, masu fama da ciwo da masu juna biyu, su kara mai da hankali sosai, su kaucewa shan kankana da danginta da sauran 'ya'yan itatuwa da suka dade a fili. (Tasallah Yuan)