lafiya1509.m4a
|
Sanin kowa ne cewa, yin aiki da dare kullum yana da illa ga lafiyar bil-adama. Sakamakon wani sabon nazari da aka wallafa a jaridar kwalejin nazarin kimiyya ta kasar Amurka a kwananan baya ya shaida cewa, gwargwadon yadda mutum ya yi aiki ya kuma hutu kamar yadda aka saba, yawan karfin da wadanda su kan yi aikin dare suka yi amfani da shi a ko wace rana ya kan ragu, don haka barazanar samun kiba da suke fuskanta tana karuwa.
An yi nazari kan baligai masu koshin lafiya 14 a cikin tsawon kwanaki 6 a jere. A cikin kwanaki 2 na farko, wadannan mutane 14 sun yi aiki sannan suka hutu yadda ya kamata, sa'an nan aka sauya lokacin aikinsu da lokacin da suke hutawa, sun yi kwanaki 3 a jere suna aikin dare, suna hutawa da rana. A cikin kwanakin nan guda 6, yawan abincin da suka ci daidai ne da wanda suka saba ci yau da kullum, yayin da suka yi sa'o'o 8 suna yin barci a ko wace rana.
Masu nazari daga dakin gwaje-gwaje kan batun da ya shafi barci da yanayin jikin bil-adama da ke jami'ar Colorado ta kasar Amurka sun gano cewa, jimillar karfin da wadanda suka yi aikin dare suka yi amfani da shi a ko wace rana ta ragu da kashi 12 zuwa 16 cikin dari.
Masu nazarin suna ganin cewa, watakila raguwar karfin da aka yi amfani da shi a ko wace rana tana da nasaba da sauye-sauyen da ke shafar jikin mutanen da su kan yi aikin dare. Yin aikin dare bai yi dai-dai da tsarin jikin dan Adam ba, wato yin aikin rana sannan a hutu da dare. Idan har ya zama tilas a yi aikin dare, ba yadda za a yi, sai a yi kokarin dai-daita wadannan tsare-tsare ta yadda jikin dan-adam zai yi saurin amincewa da su
Wani abin mamaki da masu nazarin suka gano shi ne yawan kibar da aka rage a lokacin da ake barci da rana ya fi wanda aka rage a lokacin da ake barci da dare. Koda ya ke ba a san ainihin dalilin da ya sa haka ba. Amma duk da haka wadanda su kan yi aikin dare ba za su iya rage kiba ba, saboda yawan karfin da su kan yi amfani da shi a ko wace rana ta kan ragu.
To,abin tambaya a nan shi ne, yaya za a kyautata lafiyar wadanda su kan yi aikin dare? Masu nazarin sun ce, da sauran rina a kaba kafin a fid da wata shawara ko matakai kan wannan batu. Amma ma iya cewa, watakila cin abinci mai kyau yadda ya kamata da kuma motsa jiki yadda ya kamata suna daga cikin abubuwa masu muhimmanci ga lafiyar wadanda su kan yi aikin dare.(Tasallah)