lafiya1512.m4a
|
Wani sabon nazarin da aka yi a kasar Amurka ya shaida cewa, maza masu fama da cutar AIDS kan yi saurin kamuwa da ciwon zuciya, kuma yiwuwar kamuwar su da wannan cuta na karuwa ya yin da suke kara dadewa dauke da cutar ta AIDs.
Masu nazari daga jami'ar Johns Hopkins ta kasar Amurka, da sauran hukumomin nazari sun kaddamar da rahotonsu a kwanan baya, cikin mujallar "ilmin sashen duba kayan ciki", inda suka bayyana cewa, nazarin da aka yi a baya ya shaida cewa, akwai wata irin alaka a tsakanin kamuwa da cutar AIDS da kuma ciwon zuciya, amma ba a tabbatar da irin wannan alaka ba tukuna. Masu nazarin sun tantance maza 618 masu fama da cutar AIDS, da wasu maza 383 masu koshin lafiya, a kokarin tabbatar da kasancewar irin wannan alaka a tsakanin kamuwa da cutar ta AIDS da kuma ciwon zuciya.
Sakamakon nazarin nasu ya nuna cewa, maza masu fama da cutar AIDS mai tsanani kan gamu da matsalar toshewar jijiyoyi a zukatansu cikin sauri, ta yadda suke kara fuskantar barazanar kamuwa da ciwon zuciya. Haka kuma idan mazan da suka dade suna shan maganin yaki da cutar AIDS sun kara wa'adin shan maganin da suke yi da shekara guda daya, sai barazanar toshewar jijiyoyin zukatansu ya karu da kashi 9 cikin dari.
Wendy Post, wata babbar malama a jami'ar Johns Hopkins ta kasar Amurka, wadda take shugabantar wannan nazari, ta ce ci gaban aikin ba da jinya yana ta tsawaita lokacin rayukan masu fama da cutar ta AIDS, amma duk da haka a cikin wadannan mutane, wasu suna fara fuskantar sabbin matsaloli, kamar kamuwa da ciwon zuciya, don haka nazarin da suka yi kan tabbatar da alaka tsakanin kamuwa da cutar AIDS, da kuma ciwon zuciya yana da muhimmiyar ma'ana. (Tasallah)