lafiya1511.m4a
|
Idan wani ya kamu da hawan jini, yaya zai yi? To, ya zama dole ya kula da lafiyarsa da kansa yadda ya kamata. Alal misali, a sa ido da auna jini a ko wace rana, ya rika sauya maganin da ya kan sha bisa shawarar likitoci, kana a yi abubuwa kamar yadda likitoci suka bada shawara, sa'an nan a kauracewa shan maganin da ba likita ne ya amince da shi ba.
Nazarin da aka yi a kasar Birtaniya ya shaida mana cewa, bayan shekara guda mai hawan jini ya na kula da lafiyarsa da kansa, zai samu sassaucin matsalar da cutar ke haifarwa sosai, kana kuma barazanar kamuwa da ciwon zuciya da shanyewar jiki da yake fuskanta za ta ragu sosai.
Hawan jini, larura ce da ke sanya karfin gudun jini a jikin dan Adam ya kasance cikin yanayin da ya saba wa al'ada, ta yadda gudun jinin kan wuce har 140 bisa 90 bisa ma'aunin mm Hg (millimeter of mercury). Masu nazari daga jami'ar Oxford ta kasar Birtaniya sun raba 'yan Birtaniya masu fama da cutar hawan jiki su 552 zuwa rukunoni guda 2, wadanda ke cikin rukuni na A sun mai da hankali kan kulawa da lafiyarsu da kansu yadda ya kamata, yayin da wadanda suke rukuni na B suke samun jiyya kamar yadda suke yi a baya, wato auna jini a asibiti, tare da sauya maganin da suke sha bisa shawarar likita. Wadannan mutane 552 sun kasance wadanda suka taba kamuwa da shanyewar jiki, ko masu fama da ciwon zuciya, ko ciwon sukari, ko ciwon koda da dai makamantansu.
A farkon lokacin gudanar da nazarin, dukkan wadannan masu fama da hawan jiki 552, matsakaicin gudun jininsu kan wuce ya kai 144 bisa ma'aunin mm Hg (millimeter of mercury). Amma bayan shekara guda, matsakaicin gudun jinin wadanda suka kula da lafiyarsu da kansu, ya sauka zuwa 128 bisa ma'aunin mm Hg (millimeter of mercury), yayin da matsakaicin gudun jinin wadanda suka samu jiyya kamar yadda aka saba ya tsaya a 138 bisa ma'aunin mm Hg (millimeter of mercury).
Har wa yau kuma, barazanar kamuwa da ciwon zuciya, da shanyewar jiki, da wadanda suka kula da lafiyarsu da kansu suke fuskanta ita ma ta ragu.
Masu nazarin sun ba da shawarar cewa, idan masu fama da hawan jiki sun kamu da ciwon zuciya, ko shanyewar jiki da dai makamantansu, to, ya kamata su dauki wajibabbun matakai da kashin kansu. Alal misali, su rika tattaunawa da likitoci domin tsara wani cikakken shirin samun jiyya tare, da sa ido wajen auna jini a kowace rana, tare da sauya maganin da suke sha cikin lokaci bisa shawarar likita. (Tasallah)