in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taimakawa dan Adam son cin abinci mai gina jiki ta hanyar horas da kwakwalwarsa
2015-03-23 07:45:16 cri


Kowa ya sani cewa, cin abinci mai gina jiki yana da amfani wajen kasancewa cikin koshin lafiya. Amma ga alama, abinci maras gina jiki ya fi jan hankali mutane da dama.

Sakamakon wani sabon nazari da aka fitar cikin mujallar "abubuwa masu gina jiki da ciwon sukari" ta kasar Birtaniya a kwanan baya, ya nuna cewa hakika, horaswar musamman na iya sauya abincin da mutane suke da sha'awar ci, har ta kai mutane sun rungumi kyakkyawar al'adar cin abinci, a kuma iya zage barazanar samun kiba.

Son cin soyayyen dankali a maimakon burodin garin alkama, ko halayya ce ta dan Adam tun asali? Masu nazari daga wasu jami'o'in kasar Amurka sun fara nazarinsu domin amsa wannan tambaya. Inda suka kaddamar da wani aikin horaswa na musamman don sauya abincin da mutane suke son ci.

Da farko sun tattara masu kiba, ko wadanda nauyin jikinsu ya wuce misali su 13, suka tsara wani shirin rage kiba ga wasu 8 daga cikinsu, ciki hadda aikin horaswa na sauya hali, ta yadda wadannan mutane za su rika cin abincin da ke da yawan abubuwa masu gina jiki wato Protein, da abubuwa masu taimakawa narkadda abinci wato fiber, amma ba shi da sukari mai yawa da dai sauransu.

Sauran mutanen 5 kuwa, ba a sauya musu yanayin zaman rayuwarsu na yau da kullum, da abincin da suke ci ba.

Masu nazarin sun dauki watanni 6 suna gudanar da wannan aiki. Kafin nazarin da kuma bayan nazarin, sun dauki hoton kwakwalwar wadannan rukunoni 2, musamman ma kan martanin da sassan kwakwalwar mutanen ke mayarwa game da cin abinci iri daban daban.

Manazartan sun gano cewa, bayan samun horo na tsawon watannin 6, wadannan mutane 8 dake cin abinci mai gina jiki, sun kara nuna sha'awa ga abinci mai gina jiki, a maimakon abinci maras gina jiki, yayin da sauran 5 kuma suka ci gaba da rayuwa kamar yadda suka saba a baya.

Masu nazarin sun ce, a halin da ake ciki, abinci maras gina jiki, da kuma tallace-tallacen da ake yi kansu a ko ina, su na hana mutane yin zabin da ya dace.

Amma duk da haka binciken da suka yi ya nuna cewa, idan mutane sun sauya hanyar rayuwarsu bisa radin kan su, sun kuma nisanci abinci maras gina jiki, a hankali a hankali kwakwalwarsu na iya sabawa da irin wannan sauyi, ta yadda za su saba da sha'awar cin abinci mai gina jiki, kamar kayan lambu, da 'ya'yan itatuwa, da hatsi.

Masu binciken sun ce a nan gaba, za su gudanar da wani nazari a kan karin wasu mutanen na daban don tabbatar da sakamakon nazarin da suka yi. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China