in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hirar malam Bako da wani dan wasa dan kasar jamhuriyar Niger ta kara mun sha'awar rayuwa a kasar Sin
2015-04-15 09:52:09 cri

A ranar talata 14 ga watan April 2015 da yammaci, na samu zarafin sauraron hirar malam Bako da wani dan kasar jamhuriyar Niger dake buga wasan kallon kafa a kasar Sin a cikin Sin da Afirka wanda malam Bako ke jagoranta. A cikin bayaninsa yayin zantawarsa da malam Bako, ya nuna yadda baki yan kasashen ketare da yan kasar Sin sinawa ke rayuwa cikin yanci a kasar Sin. Babu shakka, kasar Sin kasa ce da mutane ke rayuwa cikin yanci da walwala kuma kasar Sin tana kiyaye hakkin dan Adam kasar Sin tana yin tir da mulkin kama-karya a dud duniya. Kasar Sin tana aiwatar da aiyukan raya kasa a kasashe masu tasowa Sin tana bin managartan tsare-tsare wajen murkushe cin hanci da rashawa a kasar Sin inda kasar Sin ta cimma manyan nasarori masu yawa bisa yaki da cin hanci a kasar Sin. Agaskiya shirin Sin da Afirka yana kara wa milyoyin yan Afirka ilmi da karin fahimta adangane da kyakkyawar huldar diplomasiyya da cinikaiya dake akwai tsanin sabuwar nahiyar Sin ta zamani da kasashenmu na Afirka masu tasowa. Godiya ta masamman ga malam Bako jagoran shirin Sin da Afirka da kuma ma'aikatan sashin Hausa na Radiyo kasar Sin bisa kokarinsu na kara wayin kai ga al'ummar Afirka adangane da huldar diplomasiyya da cinikaiya dake wanzuwa tsakanin Sin da Afirka.

Daga mai sauraronku a kullum, Alhaji Ali kiraji Gashua.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China