in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Barcin rana na taimakawa yaran da ba su shiga makarantar firamare ba
2015-02-25 19:16:45 cri


Wani sabon nazarin da aka yi a kasar Amurka ya nuna cewa, yin barcin rana bayan cin abincin rana yana taimakawa yaran da ba su shiga makarantar firamare ba, iya haddace abubuwan da suka karatu da safe. Masu nazari sun yi nuni da cewa, lamarin ya shaida cewa, yin barcin rana na da muhimmanci sosai ga yaran da ba su shiga makarantar firamare ba tukuna.

Don haka ne binciken ya nuna cewa kamata ya yi a samar da kyakkyawan yanayi na karfafa gwiwar wannan aji na yara, wajen samun yin barcin rana.

Masu nazari daga cibiyar Amherst dake jami'ar Massachusetts ta kasar Amurka, sun fidda rahoton binciken ne a kwanan baya, a jaridar kwalejin nazarin kimiyya ta kasar Amurka, wanda ya nuna cewa yawancin mutane ba su san muhimmancin barcin rana ga kananan yara ba. Wanda Hakan ya sanya wasu hukumomin ilmantar da yaran da ba su shiga makarantar firamare a kasar ta Amurka, sun fara soke barcin rana, da nufin tsawaita lokacin karatun yaran.

Masu nazarin sun tattara yara 40 da ba su shiga makarantar firamare ba tukuna, suka bukace su su haddace wasu abubuwa da safe, daga baya sun jarraba su a karo na farko, sa'an nan da yamma suka sake jarraba su.

Masu nazarin sun gano cewa, ko da yake wadannan yara ba su da bambanci a sakamakon jarrabawar farko, amma wadanda suka yi barcin rana sun fi wadanda ba su yi barcin ba iya haddace abubuwan da aka koya musu.

Har wa yau, yaran da suka yi barcin rana sun fi wadanda ba su yi barcin ba, samun nasara matuka a cikin jarrabawar da aka yi a kashegari, lamarin da ya nuna cewa, ko da yake yaran sun yi barci da dare, amma fa'idar da yaran suka samu daga yin barci da dare, ba ta iya maye fa'idar da suka samu daga yin barcin rana ba.

Masu nazarin sun bayyana cewa, nazarin ya samar da shaida wajen tabbatar da muhimmancin yin barcin rana ga yaran da ba su shiga makarantar firamare ba tukuna. Sabili da haka kamata ya yi a bar yaran da ba su shiga makarantar firamare ba tukuna su yi barcin rana, kana kuma ya dace a samar da kyakkyawan yanayi na karfafa gwiwarsu wajen yin barcin rana.

Bayan haka kuma, ya kamata hukumomin ba da ilmi da abin ya shafa, su fidda tsarin baiwa yaran da ba su shiga makarantar firamare ba tukuna, damar yin barcin rana yadda ya kamata, tare da ci gaba da nazari kan yadda za a ba da tabbaci, da kuma kara azama kansu wajen samun damar yin barcin rana.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China