A Najeriya an gudanar da wani gagarumin biki na tura wasu ma'aikatan kiwon lafiya 250, zuwa kasashen yammacin Afirka uku, domin taimaka musu wajen yaki da cutar Ebola, cutar da har yanzu ke ci gaba da yaduwa a wadannan kasashe. Wakilinmu Murtala da ke Najeriya ya tattara labaru a yayin bikin tare da zantawa da karamin ministan lafiya na Najeriya Dr. Khalliru Alhassan, da hamshakin attajirin nan Alhaji Aliko Dangote. Ga hirarsu.