Don Allah masu sha'awar shan kofi ku lura da cewa, wani sabon nazarin da aka yi a kasar Amurka ya yi mana gargadin cewa, shan kofi fiye da kwafuna guda 28 a ko wane mako, ko kuma shan kofi fiye da kwafuna guda 4 a ko wace rana, zai kara wa mutane mata da maza da shekarunsu ba su kai 55 a duniya ba da barazanar mutuwa matuka.
Jami'ar South Carolina ta kasar Amurka ta gabatar da rahoton nazarinta a kwanan baya cewa, ta tantace mutane fiye da dubu 40 game da yadda suka yi zaman rayuwa daga shekarar 1971 zuwa shekarar 2002. Masu nazari daga jami'ar sun gano cewa, idan mazan da shekarunsu ba su wuce 55 a duniya ba su kan sha kofi na kwafuna guda 28 a ko wane mako, to, barazanar mutuwa da suke fuskanta ta karu da kashi 56 cikin dari, yayin da irin wannan barazanar mutuwar da matan da shekarunsu ba su wuce 55 a duniya ba suke fuskanta ta karu da kashi 50 cikin dari. Amma ba a gano illar da shan kofi fiye da kima yake kawo wa wadanda shekarunsu suka wuce 55 a duniya ba tukuna.
A cikin wannan nazari, yawan kofin da ke cikin kwaf guda ya kai millilita 180 zuwa 240 wato ounce 6 zuwa 8. Masu nazarin sun tunatar da cewa, kamata ya yi wadanda su kan sha kofi da yawa su mai hankali sosai kan wannan bincike. Saboda nazarinsu ya shaida cewa, shan kofi fiye da kima a kalla yana da nasaba da karuwar barazanar mutuwa, musamman ma ga mutanen da shekarunsu ba su wuce 55 a duniya ba.
Masu nazarin sun yi karin bayani da cewa, tun can da har zuwa yanzu likitoci suna muhawara kan yadda sinadarin Caffeine yake aiki a jikin dan adam. Wasu na ganin cewa, sinadarin Caffeine na kawo illa ga lafiyar mutane, yayin da wasu suke ganin cewa, sinadarin Caffeine na amfanawa lafiyar mutane. Ko da yake nazarin da jami'ar South Carolina ta kasar Amurka ta yi bai tabbatar da dangantakar da ke tsakanin shan kofi da kuma barazanar mutuwa ba, amma ya samar da sabon ra'ayi kan yadda sinadarin Caffeine yake aiki a jikin dan adam.
To, yanzu bari mu yi tunanin yawan kofi da ya fi dacewa mutane su sha a ko wace rana! Masu nazarin sun bayyana cewa, ya zuwa yanzu babu wata hukuma ko wani likita da ya ba da wata shawara kan wannan fanni. Amma galibi dai shan kofi kadan zai fi dacewa. Nazarinsu ya shaida cewa, bai kamata yawan kofin da a kan sha a ko wane mako ya wuce kwafuna 28 ba. A ko wace rana kuma, bai kamata a sha kofi fiye da kwafuna 4 ba. Kada a sha kofi fiye da kima!(Tasallah)