A yau shirin na mu zai maida hanakali ne ga cutar nan ta Ebola wadda ke matukar barazana ga rayukan al'ummar wasu daga kasashen yammacin nahiyar Afirka, cutar da kuma ake matukar tsoron yaduwar a sauran sassan duniya.
Tun dai daga watan Febrairun shekarar 2014 da muke ciki ne wannan cuta ta Ebola ta bullo a yammacin nahiyar Afirka. Kuma sannu a hankali cikin watanni hudu kacal ta jefa matukar tsoro a zukatan al'ummun dake dukkanin fadin wannan duniya. To sai daoi abin tambaya a nan shi ne, ko wannan cutar na iya saurin kama mutanen da ke da cikin koshin lafiya cikin sauri? Kuma ya ya ta ke haifar da illa a rayuwar jama'a?. Lallai akwai bukatar mu kara sani game da wannan cuta yadda ya kamata.
Kafofin yadda labaru kan yi amfani da adadi na kiyasi, da hukumar kiwon lafiya ta kasa da kasa wato WHO ke gabatarwa, wajen lasafta adadin yawan mutanen da cutar ta Ebola ke kamawa, wato misali akwai alkaluman dake nuna cewa, yawan mutanen da ke mutuwa sakamakon harbuwa da cutar ya kai kashi 90 cikin dari daga adadin dukkan wadanda suka kamu da ita.
Sai dai fa alal hakika an samu wannan adadi ne daga tasirin bullar cutar ta Ebola a kasar Congo (Kinshasa), inda cutar ta kashe mutane mafi yawa a tarihi. Don haka bai dace a yi amfani da adadin kashi 90 cikin dari kai tsaye, ba tare da yin cikakken bayani ba. Ya kamata a yi amfani da matsakaicin yawan mutuwar mutane sakamakon cutar ta Ebola, tun bayan bullarta a karo na farko a shekarar 1976, wato kashi 60 zuwa 65 cikin dari. Game da hakan ma iya cewa cutar ta Ebola ba ta kashe mutane masu tarin yawa kamar yadda ake zato ba.
Masana sun yi nuni da cewa, ya zuwa yanzu an gano nau'o'in cutar ta Ebola guda 5, wadanda suka sha bamban sosai wajen kama mutane, sa'an nan yawan mutuwar mutane sakamakon harbuwa da su ya sha bamban sosai. Bisa labarin da kafar radiyon kasar Birtaniya wato BBC ya bayar, an ce, matsakaicin yawan mutuwar mutane sakamakon cutar Ebola a Zaire ya kai kashi 79 cikin dari, ya yin da matsakaicin yawan mutuwar mutane sakamakon cutar Ebola a Sudan ya kai kashi 54 cikin dari.
Ko da yake babu tantama yawan mutuwar mutane sakamakon kamuwa da ko wace irin cuta, da ya zarce kashi 50 cikin dari ya cancani ya tsoratar da mutane kwarai da gaske. Amma duk da haka a hannu guda in an kwatanta da yawan mutuwar da mutane ke yi sakamakon cutar cizon kare, ko ciwon zazzabin cizon sauro, za a gano cewa yawan mutuwar mutane sakamakon kamuwa da cutar ta Ebola bai kai na wadancan cututtuka ba. (Tasallah)