in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sauya halayyar rayuwa maras dacewa na iya rage barazanar zubar ciki
2014-08-18 08:30:04 cri

Wasu masu nazari daga kasar Denmark sun gabatar da sakamakon wani nazari na su, ta mujallar da akai wa lakabi da "ilimin Likita mai lura da haihuwa da abubuwa masu nasaba da hakan", inda binciken na su ya nuna cewa, idan masu juna biyu suka sauya halayyar su maras dacewa ta yau da kullum, musamman ma shan giya, da rashin yin barci kan lokaci, da daidaita kiba, hakan na iya rage musu barazanar zubar ciki kwarai da gaske.

Tun daga shekarar 1996 zuwa shekarar 2002, masu nazari daga jami'ar Copenhagen ta kasar Denmark dai sun yi bincike kan hanyar zaman rayuwa, da masu juna biyu na kasarsu su fiye da dubu 90 ke bi, wadanda kasha 3.5 cikin dari daga cikinsu juna-biyun da suke da shi ya zube, cikin makonni 22 na farkon daukar ciki.

Masu nazarin sun tantance mabambantan dalilan da suke da nasaba da zubar ciki, inda suka gano cewa, shan giya, da yin barci a makare, rashin daidaitacciyar kiba, wato karincin ta ko yawan ta, da yin aiki fiye da kima, na cikin dalilan zubewar juna-biyu. Alal misali, daukar kayayyaki masu nauyi da ya zarce giram 20 a ko wace rana, na kara barazanar zubar ciki kwarai.

Kamar dai a baya, sabon nazarin da aka yi ya shaida cewa, barazanar zubar ciki da matan da suka sami ciki bayan da shekarunsu suka kai 35 ko fiye suke fuskanta ta dan karu.

Binciken ya nuna cewa shekarun mata da kuma shan giya su ne manyan barazana a fannin zubewar ciki. Tantancewar da aka yi ta nuna cewa, idan aka sauya dukkan wadannan dalilan da suke da nasaba da karuwar barazanar zubar ciki, to, za dakile zubar cikin mata masu juna biyu da yawansu ya kai kasha 25.2 cikin dari.

Masu nazarin sun nuna cewa, sakamakon nazarinsu na fadakar da mutane cewa, za a iya yin rigakafin zubar ciki ta wasu fannoni. Wato ya zama tilas mata su bi hanyar zaman rayuwa mai dacewa kafin sun sami ciki, da kuma yayin da suke da juna biyu. Har wa yau kuma, hukumomin gwamnati da kamfanonin da suke da ma'aikata ya dace su tsara manufofi da ka'idojin da ke da alaka da hakan, a kokarin ganin masu juna biyu suna kasancewa cikin koshin lafiya da tsaro. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China