Sakamakon wani sabon nazari da aka yi a kasar Birtaniya ya bayyana cewa, cin kayayyakin lambu da 'ya'yan itatuwa a kalla iri 7 a ko wace rana, ba tare da kasala ba yana taimakawa wajen rage barazanar kamuwa da ciwon kansa, da ciwon zuciya da dai sauran cututtuka, da kuma barazanar mutuwa da wuri.
Yanzu haka dai hukumomin kiwon lafiya na kasar Birtaniya su na shawartar al'ummar kasar su, da su rika cin kayayyakin lambu da 'ya'yan itatuwa a kalla iri 5 a ko wace rana, wadanda kuma nauyin ko wanensu ya zarce giram 80. Hukumomin sun gabatar da wannan shawara ce dai bisa tanade-tanaden da ke cikin wata shawara, da hukumar kiwon lafiya ta kasa da kasa wato WHO ta gabatar.
Duk da haka, wasu masu nazari daga jami'ar London ta Birtaniya sun gabatar da rahoton nazarinsu a kan wata mujallar kasar da ke cewa, tun daga shekarar 2001 zuwa ta 2008, sun yi nazari kan yadda mutanen kasar fiye da 65000 wadanda shekarunsu suka zarce 35 a duniya masu cin abinci da kuma bayanan da aka samu daga gare su game da jinya.
Sakamakon sabon nazarin ya shaida cewa, barazanar mutuwar da wadanda su kan ci kayayyakin lambu da 'ya'yan itatuwa a kallo iri 7 a ko wace rana suke fuskanta, ta yi kasa da kashi 42 cikin dari, in an kwatanta su da takwarorinsu, wadanda su kan ci kayan lambu ko 'ya'yan itatuwa iri 1 kawai a ko wace rana.
Haka kuma wadanda su kan ci kayayyakin lambu da 'ya'yan itatuwa a kallo iri 7 a ko wace rana, ba su fuskantar babbar barazanar kamuwa da ciwon kansa, da na zuciya, da shanyewar jiki da dai makamantansu.
To ko me za mu iya ci domin kiwon lafiya mu ? Danyun kayayyakin lambu sun fi dacewa wajen kiwon lafiyar jikin mu, sa'an nan salak din kayayyakin lambu, da kuma 'ya'yan itatuwa su ma suna taimakawa sosai. Ruwan 'ya'yan itatuwa kadai ba shi da amfani. Kana cin 'ya'yan itatuwan da ke cikin gwangwani zai kara barazanar kamuwa da ciwon zuciya,
sakamakon yawan sukarin da ke cikin irin wadannan kayan gwangwanin.
Sakamakon wannan nazari ya kuma nuna mana cewa, cin 'ya'yan itatuwa da kayayyakin lambu da yawa, na taimakawa mutane kasancewa cikin koshin lafiya, tare da rage barazanar kamuwa da cututtuka da mutuwa. Ko da dai ba a iya cin 'ya'yan itatuwa da kayayyakin lambu a kalla iri 7 ba a ko wace rana, abu ne mai matukar kyau a yi kokarin cin su da dama. (Tasallah)