Sinawa kan ce, matukar bacin rai kan kawo illa ga lafiyar mutane. Kuma sakamakon wani sabon nazarin da aka gabatar a kwanan baya ya shaida cewa, hakika saurin yin fushi, ko kuma gazawa wajen kafa kyakkyawar hulda tare da sauran mutane, kan yi matukar lahanta lafiyar mutum. Binciken ya kuma nuna cewa cacar baki da abokan zama, ko abokai, ko abokan aiki sau da yawa, ko kuma fuskantar irin wannan matsin lamba a kullum, kan kusantowa masu da barazanar mutuwa da wuri bisa matsakaicin shekaru da ake hasashen zai yi a raye, musamman ma jinsin maza.
Wasu manazarta na jami'ar Copenhagen ta kasar Denmark ne dai suka gabatar da rahoton wannan bincike, a wata mujallar kasar Birtaniya, dangane da cututtuka masu yaduwa, da kiwon lafiyar al'umma, inda a cewarsu, tun daga shekara ta 2000, manazarta ke yin bincike kan 'yan Denmark 9875, da shekarunsu suka wuce 36 amma ba su kai 52 a duniya ba, a fannonin huldar da ke tsakaninsu da sauran mutane a fannin zamantakewar al'umma, da kuma barazanar mutuwa da wuri da suke fuskanta. Binciken ya nazarci kamar sau nawa ne mutanen su kan yi cacar baki da abokansu ko iyalansu, da yadda suke fuskantar matsin lamba yayin da suke ma'amala da sauran mutane, da dai makamantansu.
Bayan shekaru 11, cikin dukkan mutanen da aka bincika, mata 196, da maza 226, sun mutu sakamakon ciwon sankarau, ko ciwon zuciya, ko ciwon hanta, ko kisan kai da dai sauransu.
Sakamakon binciken dai ya nuna cewa, fuskantar matsin lamba a kullum, yayin ma'amala da da sauran mutane a zamantakewar al'umma, ko abokan zama, ko 'ya'ya, kan gabatar da bukatu da dama, wadanda kan kara barazanar mutuwa da wuri da kashi 50 cikin dari zuwa kashi 100 cikin dari.
Har wa yau yin cacar baki da sauran mutane sau da yawa, kan kara irin wannan barazana da rubi 2 zuwa rubi 3, musamman ma ga maza, da marasa ayyukan yi.
Masu nazarin sun ce, nazarin da aka yi a baya ya shaida cewa, kyakkyawar hulda a tsakanin mutum da sauran mutane, kan taimakawa kiwon lafiya. Kana nazarin ya nuna cewa, hulda maras kyau a tsakanin mutum da sauran mutane, na iya matso da barazana ga lafiya.
Ko da yake masu binciken ba su fahimci dalilin hakan ba, sai dai su na ganin koyon yadda ake sassauta matsin lamba ta tunani, ko neman taimako daga wajen likitoci masu ilimin tunani in akwai bukata, na iya taimakawa wajen rage irin wannan barazana. (Tasallah)