Wani nazarin da wata kwalejin nazarin kiwon lafiya da ke kasar Amurka ya tallafawa, ya nuna cewa, yin tattaki na tsahon mintoci 20 a kowace rana ga tsoffafin da shekarunsu suka wuce 70 amma ba su zarta 90, zai iya taimaka musu wajen ci gaba da yin tafiya ba tare da taimako ba, tare da kuma rage musu baranazar samun nakasa, ta yadda han zai kara kyautata zaman rayuwarsu sosai.
Kowa na sane da cewa, motsa jiki na taimakawa tsoffi wajen kasancewa cikin koshin lafiya. Amma babu wani tabbatacciyar shaida da ke nuna cewa, motsa jiki zai iya kare tsoffi daga samun nakasa. Sai dai wannan bincike na tafiya ba tare da wani taimako ba, bisa daukar matakin motsa jikin wata muhimmiyar alama ce ga tsoffi, da za ta iya taimaka musu samun kyuatatuwar zaman rayuwar su da kansu.
Bisa wannan sabon nazarin da aka yi, idan mun ce, tsoho na iya tafiya ba tare da wani taimako ba, hakan na nuna cewa tsohon na iya tafiya ta a kalla mita dari hudu.
Manazarta sun kaddamar da wani gwaji mai suna "Samar da babban tasiri ga yanayin zaman rayuwar tsoffafi", inda suka dauki tsoffi masu aikin sa kai 1635, da shekarunsu suka wuce 70 amma ba su kai 90 a duniya ba, wadanda kuma suke fuskantar barazanar kasa yin tafiya ba tare da wani taimako ba, sakamakon yawan zama a kejura tsahon dogon lokaci ba tare da motsawa ba, duk da haka a farkon lokacin da aka kaddamar da gwajin, irin wadannan tsoffi sun iya tafiya ta tsawon mita 400 ba tare da wani taimako ba.
Manazarta sun raba wadannan tsoffi zuwa rukunoni 2, daya mai kunshe da tsoffi 818, wadanda suka yi mintoci 150 suna tafiya a ko wane mako, tare da dan motsa jiki. Dayan kuma mai kunshe da tsoffi 817, aka koyar da su ilimin kiwon lafiya, tare da dan motsa jiki na mintoci 5 zuwa 10 a ko wane wata.
Bayan shekaru 2 da rabi, wasu tsoffi 246 dake cikin rukunin wadanda su kan yi tafiya a ko wane mako ba sa iya tafiya da ta kai tsawon mita dari 4 ba tare da taimako ba, kamar yadda wasu 290 dake cikin rukunin wadanda sukan dan motsa jiki na mintoci 5 zuwa 10 a ko wane wata suka yi.
Manazartan sun gano cewa, galibi dai wadanda ba sa yin tafiya a ko wane mako sun fi fuskantar barazarar kasa yin tafiya, idan an kwatanta su da wadanda sun kan yi tafiya a ko wane mako.
Don haka dai sakamakon wannan nazari ya nuna cewa, motsa jiki ta hanyar kimayya, ya taimaka wa tsoffi samun kasance cikin koshin lafiya, tare da rage barazanar nakasa gare su.(Tasallah)