Wata hukumar jin kai ta kasar Birtaniya mai suna "yara makafi na Birtaniya" ta gabatar da wani rahoto a kwanan baya dake kunshe da binciken da ta yi, wanda ke cewa a shekarun baya, yawan yara makafi, ko yaran da ke fama da matsalar ido a kasar ta Birtaniya ya karu sosai, lamarin da yake nasaba da karuwar yawan 'yan bakwaini da aka kubutad da su daga bakin mutuwa. Masana sun yi kira ga iyaye da likitoci da su mai da hankali kan lafiyar idanun 'yan bakwanin, a kokarin gano alamun fuskantar matsala cikin hanzari ba kuma tare da bata lokaci ba.
Hukumar ta ce ta yi cikakken nazari kan bayanai da shirin ba da hidimar kiwon lafiya na Birtaniya, da hukumar harkokin kididdigar kasar, da sauran hukumomin kasar suka tattara, ta kuma yi bincike kan yara 130 da ke fama da matsalar ido da kuma iyayensu. Sakamakon binciken na su ya shaida cewa, tun daga shekarar 2006 har zuwa shekarar nana ta 2014, yawan yaran makafi ko yaran da ke fama da matsalar ido, wadanda suka yi rajista ya karu da kashi 9 cikin dari, musamman ma a cikin wadanda shekarunsu ba su wuce 5 a duniya ba, irin wannan karuwa ta kai kashi 12 cikin dari.
Rahoton na ganin cewa, irin wannan karuwa mai tada hankali na da nasaba da karuwar yawan 'yan bakwainin da aka kubutad da su daga bakin mutuwa. Har wa yau wannan rahoto ya nuna cewa gwargwadon saurin haifuwar 'yan bakwaini, gwargwadon matsalar ido da zai iya gamuwa da ita. An kiyasta cewa, a shekaru 10 da suka gabata, yawan 'yan bakwaini, da tsawon lokacin da suke kasancewa a mahaifansu bai wuce makonni 26 ba, kuma fama da suke yi da matsalar ido ya karu da kashi 22 cikin dari.
Har wa yau binciken ya nuna cewa, iyaye da likitoci ba su gano matsalolin ido da yawancin yara suke fama da su cikin lokaci ba. Kimanin rubu'in iyaye sun ce, sai bayan da 'ya'yansu suka gamu da matsalar ido har shekara guda ko fiye da haka ne, suka kai su asibiti domin a yi musu magani.
Masana daga hukumar ta jin kai ta Birtaniya mai suna "yara makafi na Birtaniya" sun yi gargadin cewa, ya zama wajibi iyaye da likitoci su mai da hankali kan lafiyar idanun kananan yara, musamman ma 'yan bakwaini, su lura da alamun da watakila suke iya bayyana abkuwar matsalar ido, kamar idanun kananan yara su yi ja, ko yawan murza idanu da yara ke yi, ko kuma ba su mayar da martani kan hashe idan sun kalla ba. (Tasallah)