logo

HAUSA

Shugabannin IPC da BOCOG sun bayyana kwarin gwiwar gudanar da gasar nakasassu ta lokacin sanyi

2022-02-28 10:32:34 CRI

Shugabannin IPC da BOCOG sun bayyana kwarin gwiwar gudanar da gasar nakasassu ta lokacin sanyi_fororder_220228-Olympics-Ahmad2

Shugaban kwamitin shirya gasar wasannin nakasassu ta lokacin hunturu ta Beijing 2022, BOCOG, Cai Qi, da takwaransa na kwamitin shirya gasar wasannin nakasassu ta lokacin hunturu ta kasa da kasa (IPC), Andrew Parsons, sun tattauna game da shirye-shiryen gasar ta Paralympics ta lokacin hunturu dake tafe, inda suka bayyana kwarin gwiwar samun nasarar gudanar da gasar a yayin da suka tattauna ta kafar bidiyo a ranar Lahadi.

Cai, ya godewa kwamitin IPC, bisa goyon bayan da yake baiwa kwamitin shirya gasar Beijing Paralympic ta lokacin sanyi, inda ya bayyana cewa, an gudanar da shirye-shiryen gasar wasannin Olympics da Paralympics a bisa tsari iri guda, wanda ya yi daidai da manufar karbar bakuncin gasar ta hanyar amfani da makamashi mai tsafta, da shigar da kowane bangare, da kuma bude kofa, da aiwatar da wasannin bisa tsari mai inganci.

Cai ya kara da cewa, za a ci gaba da daukar matakan dakile annobar COVID-19 a yayin gasar ajin nakassasu ta lokacin sanyi, kwatankwacin wadanda aka yi amfani da su a lokacin gasar Olympics ta lokacin sanyi. Ya ce za su ci gaba da bada fifiko wajen lura da cibiyoyin wasannin tare da daukar bukatun mahalarta gasar da matukar muhimmanci.

Ya ce, “muna fatan IPC da BOCOG, za su yi aiki tare, domin tabbatar da ganin mahalarta gasar sun kiyaye ka’idojin yaki da annobar, kuma sun  nuna juriya, domin cimma nasarar gudanar da gasar wasannin motsa jiki ta lokacin sanyi ta nakassasu cikin nasara. (Ahmad)