logo

HAUSA

Wakilin kasar Sin: Ya kamata duk wani mataki da kwamitin sulhu zai dauka ya zama mafita ta hanyar diflomasiyya ga rikicin Ukraine

2022-02-28 11:23:24 CRI

Wakilin kasar Sin: Ya kamata duk wani mataki da kwamitin sulhu zai dauka ya zama mafita ta hanyar diflomasiyya ga rikicin Ukraine_fororder_220228-Zhang Jun Ukraine-Faeza2

Kwamitin Sulhu na MDD ya amince da wani kuduri mai lamba 2623, da ya yi kira da wani taro na musamman na babban zauren MDD, domin nazari da gabatar da shawarwari game da matakin da ya kamata a dauka kan rikicin Ukraine. Wannan shi ne karo na farko cikin shekaru 40, da kwamitin ya amince da irin wannan kuduri. Sai dai, kasashen Sin da Indiya da Hadaddiyar Daular Larabawa sun kauracewa kada kuri’a.

Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya yi bayani game da kuri’arsa, inda ya ce Sin ta yi ammana cewa abu mafi muhimmanci a yanzu shi ne, dukkan bangarori su kai zuciya nesa tare da kaucewa ta’azzarar yanayin Ukraine. Ya ce kasar Sin na goyon baya tare da karfafa gwiwar warware rikicin cikin lumana, kana tana maraba da hawan teburin sulhu kai tsaye ba tare da bata lokaci ba, da kuma yarjejeniya tsakanin Rasha da Ukraine. A lokaci guda kuma, tana goyon bayan bangaren Turai da kuma Rasha, su tattauna kan batun tsaron yankin Turai bisa adalci da daukaka tabbatar da tsaro a dunkule, ta yadda a karshe za a samu wani tsarin tsaro a Turai mai inganci da dorewa da kuma daidaito.

Bugu da kari, ya ce kasar Sin ta yi ammana cewa, kwamitin sulhu zai bayar da fifiko ga tsaro da kwanciyar hankalin yankin da kuma tsaro na bai daya ga dukkan kasashe, tare da taka muhimmiyar rawa wajen warware rikicin Ukraine. (Fa’iza Mustapha)