logo

HAUSA

Yan bindiga sun kashe mutum 3 a tsakiyar Najeriya

2022-02-28 09:38:39 CRI

A kalla mutane uku aka kashe da safiyar ranar Lahadi, a sanadiyyar harin da ’yan bindiga suka kaddamar a wasu kauyukan jihar Naija, dake shiyyar tsakiyar Najeriya.

Babban jami’in hukumar ’yan sanda jihar Naija, Monday Bala Kuryas, ya fadawa ’yan jaridu a Minna, babban birnin jihar cewa, ’yan sanda sun kaddamar da bincike da kuma farautar ’yan bindigar wadanda suka yi amfani da babura inda suka afkawa kauyukan Ebbo, da Ndagbegi, dake yankin karamar hukumar Lavun a jihar.

Kuryas ya ce, kawo yanzu ba a san takamamman dalilin kaddamar da hare-haren ba, inda ya bayyana cewa, ’yan bindigar sun kai wa kauyukan farmaki ne da misalin karfe 5 na safe agogon wurin, inda suka aikata mummunan aikin.

A cewar jami’in, an tura rundunar ’yan sandan musamman da sojoji zuwa yankunan, kuma sun kaddamar da bincike da nufin farauto bata-garin da suka kaddamar da harin. (Ahmad)