logo

HAUSA

Wang Yi: Bai kamata duniyarmu ta sake rufe kofa ba

2022-02-28 14:22:26 CRI

Wang Yi: Bai kamata duniyarmu ta sake rufe kofa ba_fororder_wang yi

Yau Litinin mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya gabatar da wani rahoto ta kafar bidiyo yayin babban taron tunawa da cika shekaru 50 da sanar da “hadadden rahoton Shanghai” tsakanin gwamnatocin kasashen Sin da Amurka, inda ya bayyana cewa, bai kamata a sake rufe kofa ba, saboda an riga an bude kofa ga juna, haka kuma bai kamata a sake shiga yaki ba, saboda an riga an kawo karshen yakin cacar baka, ya dace sassan biyu su yi kokarin neman hanyar da ta dace yayin da suke daidaita huldar dake tsakaninsu a sabon yanayin da ake ciki, ta yadda al’ummun kasashen biyu, za su ci gajiya.

Abu mafi muhimmanci shi ne, a martaba manufar kasar Sin daya kacal a duniya, kana a yi martaba da juna, ban da haka sassan biyu su nace kan manufar yin hadin gwiwa domin samun ci gaba tare, na hudu, kasashen biyu su sauke nauyin dake wuyansu a matsayinsu na manyan kasashe a duniya, domin samar da karin tallafi ga duniya baki daya.(Jamila)